• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

A Ƙarshe Gwamnatin Buhari Zata Soke Kungiyar ASUU

ByLucky Murakami

Aug 23, 2022

Kamar yadda binciken mu ya gano alamu sun bayyana a jiya cewa gwamnatin tarayya na iya duba yiwuwar haramta kungiyar malaman jami’o’i, ASUU idan har ta kasa janye yajin aikin da ta dade bayan tayi mata tayin dakatar da shi.

Gwamnatin tarayya ta kuma amince da karin Naira biliyan 100 ga bangaren jami’o’in a wani bangare na fahimtar juna da sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009.

Baya ga haka, an amince da Naira biliyan 50 daidai da yadda kungiyoyin da ke jami’o’i za su raba a matsayin alawus-alawus.

Kungiyoyin hudu na jami’o’i da ke takun-saka kan biyan kudaden alawus-alawus din su ne ASUU, wacce ta kira nata kudaden da ake ba su albashi, da manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU, kungiyar ma’aikatan da ba malamai ba ta, NASU da Ƙungiyar Ƙwararrun, NAAT.

Zan Mayar Da Jami’o’i Karkashin Kulawar Gwamnatocin Jihohi Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a bababr jam’iyyar PDP, Atiki Abubakar, ya lashi takobin mika wa gwamnatocin jihohin ragamar kulawa da Jami’o’in gwamantin tarayyar, idan ya lashe zaben 2023.

Atiku, ya bayyana haka ne yayin wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a Jihar Legas.

An ruwaito Atiku ya ce kadarorin da Najeriya ta mallaka na iya karewa nan ba da dadewa ba.

“Daya daga cikin abubuwan da na shirya yi shi ne karfafa wa bangaren ‘yan kasuwa na cikin gida da na waje da su zuba jari a banagren ilimi domin Najeriya ba ta da kadarorin da za su dade tana sarrafa su kamar yadda take yi a yanzu.”

Ya kuma yi tsokaci kan talaucin da ya addabi yawancin ‘yan kasar, inda ya ce “tun bayan da Najeriya ta koma bisa turbar dimokradiyya a 1998 zuwa 1999, kasar ba ta taba samun kanta cikin tasko kamar wanda ta ke ciki ba a yanzu.”

Atiku ya yi alkawura da dama kan sauya wasu fasali na kadarorin Najeriya ciki har da sayar da Babban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC).

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

One thought on “A Ƙarshe Gwamnatin Buhari Zata Soke Kungiyar ASUU”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *