Karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin kawo karshen yajin aikin malaman jami’a (ASUU) nan bada jimawa ba.
Ministan ya bayar da tabbacin ne a Owerri, babban
birnin jihar Imo a karshen mako yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a yayin wani liyafa da abokansa suka shirya masa.
Ya ce:
“Zan iya tabbatar maku cewa gwamnati ta damu sosai game da lamarin. Har yanzu da nake magana da ku tunane-tunane da dama, tattaunawa da dama da taruka na gudana da nufin magance lamarin cikin gaggawa.”
Ya bayyana fatansa cewa za a kawo karshen rashin jituwa nan ba da jimawa ba, jaridar The Nation ta rahoto.
Ya kara da cewa:
“Ina kyautata zaton cewa za a magance rashin jituwar da ke tsakanin gwamnati da malaman ASUU nan ba da jimawa ba domin yaranmu su koma makaranta.”
Ministan ya ce matsalolin da ke ma’aikatar ilimi na da wuyar gaske kuma gwamnatin tarayya bata yi kasa a gwiwa ba wajen neman mafita da kawo karshen yajin aikin kungiyar ASUU.
Ya ce a shirye yake ya bayar da gagarumin gudunmawa a ma’aikatar ta hanyar aiki tare da ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, rahoton The Cable.
Ya ce:
“A shirye nake na bayar da gudunmawa a ma’aikatar da bangaren ilimi ta hanyar aiki tare da ministan, Mallam Adamu Adamu. A duk inda matsaloli suke dole akwai mafita. Kuma ina iya tabbatar maku cewa za mu nemo mafita kuma yaranmu za su koma makaranta.”