• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

A Karshe An Maka Ado Gwanja, Mr 442, Safara’u, Da ‘Yan Matan TikTok A Kotu

ByLucky Murakami

Sep 7, 2022

Kamar yadda muka kawo muku labari kwanakin baya wanda wani shahararren lauya dake zaune a birnin Kano maisuna Badamasi Sulaiman Gandu ya shigar da karar mawaki Ado Gwanja kan cewar mawakin yana lalata tarbiya.

Cikin takardar korafin lauyan ya bukaci gwamnati ta dauki babban mataki ga Ado Gwanja akan wannan sabuwar wakar tasa maisuna “CHASS” dayayi.

Haka zalika barrister ya mika takardar ga Hukumar Hisba, sannan ya sake mika takardar ga hukumar tace fina finai ta jhar kano kan cewar yakamata a dauki mataki akan mawakin, a cewarsa jahar kano tanada tsari da mutunta addini amman saigashi wani mawakin yana wargaza tarbiyar yan jahar Kano.

Hallau dai labarin da amihad.com take samu a yau shine an maka shahararrun mawaƙan zamani na Arewa da fitattun jaruman TikTok a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke yankin Bichi a Kano bisa zargin rashin tarbiyya.

Duk da cewa majiryarmu DAILY NIGERIAN Hausa ba ta samu kwafin ƙarar ba, amma majiyoyi sun ce laifuffukan sun haɗa da wakokin rashin tarbiyya da rawar TikTok da ke da alaƙa da lalata tarbiyyar al’umma.

Sai dai majiyar tamu DAILY NIGERIAN ta samu kwafin wasikar da kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa ƴan sanda na neman a binciki koke-koken da ke gaban masu gabatar da ƙara.

Wadanda aka zayyana a wasikar da aka aika wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano sun hada da Mr 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Murja Kunya, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiyana.

 

“Sakamakon karar da Muhd ​​Ali Hamza Esq, Abba Mahmud, Esq, Sunusi I. Umar Esq, Abba, A.T Bebeji Esq, B.I Usman Esq, Muhd ​​Nasir Esq, L.T Dayi Esq, G.A Badawi & Badamasi Suleiman Gandu Esq su ka gabatar.

“Alkali mai shari’a na Babbar Kotun Shari’a na Bichi a Kano ya umurce ni da in rubuta tare da neman ku da ku gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin a sama domin daukar matakin da ya dace.

“An maƙala kwafin takardar korafin don ƙarin bayani. Ka huta lafiya,” in ji wasiƙar, wacce rijistaran kotun, Aminu Muhd ​​ya sanya wa hannu.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *