Kamar yadda rahoto ya tabbatar mana babban lauuyan gwamnatin Jihar Sakkwato kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Sulaiman Usman (SAN), ya karbi ragamar gudanar da shari’ar da aka shigar a na karar Aliyu Sanusi Umar wanda ya kade daliba Fatima Sulaiman ‘yar shekaru 16 wanda hakan ya zama silar yanke mata kafa.
Jaridar Leadership ta rawaito cewa an gurfanar da Umar ne a gaban Babbar Kotun Majistare da ke Arkilla a bisa ga tukin ganganci, tuki
ba tare da lasisi ba tare da yi wa Fatima babbar illa a gaban makarantusu bayan ta kammala rubuta jarabawar karshe.
A zaman kotun a jiya, Babban Lauyan Gwamnati, a baki ya bukaci kotun da ta ba shi damar karbar shari’ar bisa ga dogaro da sashe na 211 na tsarin mulkin Kasa na 1999 da kuma sashe na 106 na Kundin dokar shari’a ta Jihar Sakkwato.
Babban Lauyan Gwamnatin wanda ya samu wakilcin Barista Sufyanu Umar Mai- Kulki ya bayyana cewar kundin dokokin da ya gabatar, sun bash
i damar karbar ragamar duk wata shari’ar miyagun laifuka wadda wani ko wata Hukuma ta shigar.
Haka ma Lauyan ya bukaci kotun da ta dage sauraren shari’ar zuwa mako daya domin ba shi damar shiryawa shari’ar yadda ya kamata.
Sai dai Lauyan mai kariya, Jacob Ochidi (SAN) ya nuna rashin aminta da bukatar karbar shari’ar a baki yana cewar tun farko kotu ta aminta da gudanar da sauri a shari’ar daga ranar Talata. Ya ce idan har ba za a gaggauta shari’ar ba, to a bayar da belin wanda yake kariya domin a cewarsa ga alamu za a tsawaita shari’ar.
Da take yanke hukunci kan matsayar kotu, Mariya Haruna Dogon-Da
ji ta sa kafa ta yi fatali da bukatar bayar da wanda ke kariya beli ta na cewar an yi sauri idan aka bayar da belinsa a wannan lokacin. A kan wannan ta dage zaman kotun zuwa ranar 19 ga Satumba tare da bayar da umurnin ci-gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyara hali.