• Thu. Sep 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Abin Mamaki Baya Karewa Wani Mutum Yayiwa Mata 102 Ciki Shi Kadai

ByLucky Murakami

Aug 24, 2022

A kullum fadi tashin shafin amihad.com shine ta kawo muku labaran da zaku kayatar daku masu burgewa da ban mamaki.

A wannan karon mun kawo muku labarin yadda wani bawan Allah ya haifi ‘Ya’ya sama da 100 kamar yadda mu ka samu labari daga wata Jaridar kasar waje.

Labarin wani mutumi ya zo mana game sa wani mutumi da ya samu yara sama da 100 a Duniya.

Wannan bawan Allah ya rika bada kwayan haihuwar sa ne a asibiti ga wadanda su ke bukatar haihuwa ba tare saduwa da namiji ba.

Sai dai wannan mutumi ya saba dokar da ke Kasar Netherlands na bada ruwan namiji a asibiti.

Wannan mutumi ya bada ruwan na sa a asibitocin kasar har 11 inda yace shi so yake ya ga a sanadiyyar sa an samu yara da dama a Duniya wanda hakan na burge sa.

Kwanakin baya in baku manta ba mun kaewo muku yadda akayi hira da wani mutumi ‘Dan kasar Ghana da ya haifi ‘ya ‘ya fiye da 100 a Duniya kuma yace har yanzu bai gaji da samun yaran ba.

Wanda wannan labari ya bawa mutane mamaki matuka har sukai ta ajiye ra’ayoyinsu.

 

Hisbah ta kori babban jami’inta da aka samu da matar aure a Otal

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kori babban jami’in ta Sani Nasidi Uba Rimo da aka samu da matar aure a ɗakin Otal.

Hakan na cikin wata takarda da hukumar Hisbar ta aike wa Freedom Radio mai ɗauke da sa hannun babban jami’in mai lura da ma’aikatan hukumar Malam Sani Alasan.

Sanarwar ta ce, korar Rimo ta biyo bayan karɓar rahoton Kwamitin bincike kan zargin da aka yi masa da hukumar ta yi.

Sakamakon binciken kwamitin, la’akari da faruwar lamarin ya sanya tilas Hisbah ta ɗauki wannan mataki na korar sa daga aiki.

A watannin baya ne dai aka zargi Sani Nasidi Rimi da ɗaukar wata matar aure tare da kai ta wani ɗakin Otal a unguwar Sabon Gari.

Zargin da Rimon ya tabbatar da aikatawa yana mai cewa ya yi hakan ne domin ya gargaɗi mijinta.

Daga nan ne kuma rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta fito ta wanke Rimon, inda ta ce, eh haka ne ya kai ta Otal amma don ya tseratar da ita.

Sai dai kuma wannan bayani na ƴan sanda ya ci karo da sakamakon rahoton da kwamitin hukumar Hisbah ya fitar, bayan shafe tsawon lokaci yana ƙwaƙƙwaran bincike a kan lamarin.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

One thought on “Abin Mamaki Baya Karewa Wani Mutum Yayiwa Mata 102 Ciki Shi Kadai”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *