Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Abin Tausayi Yadda Hukumomin Saudiyya Ke Wulakanta Alhazan Najeriya

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiJuly 11, 2022No Comments2 Mins Read

    Wasu Alhazan sun yi zargin cewa an nuna musu bambanci a zaman da aka yi na Muzdalifa, a lokacin aikin Hajjin na bana a Saudiyya.
    Alhazan Najeriya da ke sauke farali a kasa mai tsarki sun koka da yadda hukumomin Saudiyya ke ‘wulakanta’ su ta hanyar mayar da su saniyar ware a wasu bangarori yayin aikin Hajjin bana.

    Wadanda BBC ta zanta da su sun ce akwai bambanci tsakanin abubuwan da hukumomin na Saudiyya ke tanadar wa alhazan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba.

    Daya daga cikinsu, Abubakar Baban Gwale, ya ce “A filin Muzdalifa za ka ga a wurin wasu kasashen akwai shimfida, amma mu [Najeriya] babu shimfida, sai dai ka nemo kwali ka kwanta a kai.”

    Dama dai alhazan na kokawa kan gazawar hukumomi wurin tanadar musu da abubuwan bukata yadda ya kamata.

    Sun yi zargin cewa akwai karancin masu kula da lafiyarsu da kuma abinci.

    Mahajjatan sun ce a duk lokacin da suka koma tantunan kwanansu daga wurin jifan shaidan (Jamrah), ba sa samun abincin da ya kamata.

    Wata Hajiya da ita ma BBC ta zanta da ita, ta ce a kullum shinkafa ake ba su, sannan ba a tanadi abinci na masu lalurar ciwon suga ba.

    Bugu da kari ta ce babu tuwo, wanda shi suka fi bukata idan aka kwatanta da sauran abinci.

    Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ya tabbatar da matsalar.

    Ya ce laifin na cibiyar da take kula da dawainiyar alhazai ce ta Saudiyya wadda ake kira Mu’assasa.

    Ya kuma ce Hukumar Alhazan ta Najeriya ta rubuta koke kan batun.

    Haka nan hukumar ta bukaci a biya Najeriya kudaden da ta bayar a bangaren abinci, kasancewar ba a samar da abincin da ya kamata ba.

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.