• Mon. Jun 17th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Abinda Matan Kannywood Sukai A Gidan Gwamnati Ya Jawo Cece-kuce

ByLucky Murakami

Jul 25, 2022

Abinda Matan Kannywood sukai a gidan gwamnati ya jawo abun magana ta inda mutane suketa maganganu kala kala akai.

An hangi fiskokin manyan jaruman kannywood a gidan gwamnati shin kome sukaje yi Allah masani sai dai kuma ba abin mamaki bane dan an hangesu achan din domin daman suna yiwa gwamnati aiki.

Manyan jaruman kannywood din dai sunyi gangami izuwa gidan gwamnatin jihar Kano donmin tattaunawa da gwamna da kuma matar sa a ofishin gwanma dake government house.

Anga hutunan su irin su rukayya dawayya dasu fati shu’uma dadai sauran masu ruwa da tsaki acikin masana’antar kannywood ta Kano.

[ads1]

Daman kuma ana cewa duk wata gwamnati dazata kafa mulki saita nemi goyon bayan yan kannywood din domin suyi mata kamfen acikin finafinai da kuma wakoki don ana ganin suna da dinbim masoya kuma suna da kafa me karfi wacce idan suka tura sako yakan game ko ina shi yasa duk gwamnatin da zata zo takanyi kokarin hada kai dasu.

Duk da zagin da suke sha awajen al’umma na cewa suna ganin gwamnati tanayin ba daidai ba amma ba zasu iya tsawatar mata ba kusu ankarar da ita ta wata hanya ba amma idan zuwa karbo kudi ne sun iya hada kai suje.

Ana ganinda suma matan masana’antar kannywood din kawai kansu suka sani babu ruwansu dame ya damu al’umma.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *