Wani bidiyo da yake yawo a kafafen sada zumunta yasa malam yayi martani mai zafi cikin bacin rai.
Da zarar an ambaci wayar salula abin da ke fara zuwa zukatan mutane shi ne, wata na’urar zamani mai saukaka isar da sako.
Ko dai ta hanyar sakon kar ta kwana, ko kiran gaggawa a fadi wani abu da a baya sai an dauki tsawon kwanaki kafin sakon ya isa inda ake bukata.
Wasu kuma za su iya kallon wayar salula a matsayin jakadiyar sada zumunci, ko ma ‘yar aiken da isarta da wuri ka iya ceto rayuwar wani ko wasu mutane daga fadawa wani ibtila’i.
Misali gobara, hadarin mota, rashin lafiya, kwantar da tarzoma, isar da sakon farin ciki ko akasin haka.
A takaice wayar salula na taka muhimmiyar rawa a rayuwarmu ta yau da kullum.
https://youtu.be/2HEPOS-e9BQ