• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Abubuwan Da Baku Sani Ba Akan Lamarin Ummita Wanda Dan China Ya Kasheta

ByLucky Murakami

Sep 23, 2022

A makon da ya gabata ne wata budurwa mai suna Ummulkuthum Sani Buhari wadda take zaune da iyayenta a rukunin Unguwar Janbulo da ke yankin karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano ta gamu da ajalinta lokacin da wani dan kasar China mai suna Geng Kwaron ya farmake ta har gidansu, inda ya samu nasarar daddaba mata wuka.

Binciken da mahiyarmu Jaridar Leadership Hausa ta gudanar kan lamarin ya gano cewa, Mista Geng da Ummulkulthum sun dauki wani lokaci suna soyayya, amma daga bisani ya sami labarin ta yi aure kamar yadda ya fada, don haka ya yi fushi ya je gidansu.

Faruwar lamarin ke da wuya aka garzaya da ita wani asibiti mai zaman kansa da ke Kano, inda nan take ta ce ga garinku.

Ita dai wannan marigayiyar sunanta Ummulkulthum amma an fi kiran ta da Ummita, ta gama karatun digiri a fannin aikin gona daga jami’ar Kampala da ke Uganda, inda yanzu haka tana bautar kasa a Sakwato.

Kamar yadda wata majiya ta tsegunta mana, bayan samun labarin wannan kisan gilla, jama’a sun taso domin lakadawa wannan mai tabargaza duka, sai jami’an kula da shige da fice tare da jami’an ‘yan sanda suka kwace shi daga hannun mutanen da suka fara sassama shi.

Majiyarmu ta binciko cewa marigayiyar ta hadu da wannan dan kasar China a kantin Shoprite da ke kan titin zuwa gidan adana namun daji (Zoo) lokacin da ta je sayan turare.

Tun daga nan suka shiga soyayya, kawayenta da aminanta duk sun tabbatar mana da cewa kawartasu ta yi wa Mista Geng alkawarin za ta aure shi, amma daga baya wani dalili ya faru ba su yi aure ba ta auri wani daban.

Bayan Ummita ta yi aure ne kuma sai auren nata ya mutu ta dawo gidansu, daganan wannan dan kasar China ya samu labari ya dawo a kan a ci gaba da soyayya da ita kuma sai ta dinga kin saurarensa.

Da take yi wa manema labarai karin haske kan lamarin, mahaifiyar Ummita ta ce tabbas ita ma ta san shi, domin ya dade yana zuwa yana son ya ga Ummita amma ta ki fitowa.

“Ranar Juma’ar da ya zo yana buga kofa sai na je ya bude masa kofa, ai kuwa yana shigowa ya bankade ni, ya yi kan Ummita ya caccaka mata wuka har sai da ta mutu.

“Babu irin ihun da ban yi ba, kuma gashi daga ita sai sauran ‘yan’uwanta mata, domin babansu ya rasu, sannan yayanta namiji ya fita kuma a wannan lokacin ana ta ruwan sama, babu mutane da kyar wani mutum ya kawo mana dauki kafin daga bisani mutane suka kawo dauki bayan da mai afkuwa ta afku.”

Mahaifiyar ta Ummita ta ce yanzu haka yana hannun hukuma, kuma tana fatan hukuma ta bi mata hakkin yarinyarta da wannan mutumin ya kashe ta har gida.

Da aka tambayi mahifiyar marigayyar shinko ta san da wani alkawari a tsakaninsu?

Sai ta ce, tabbas Ummita ta taba cewa za ta aure shi kafin ta auri tsohon mijinta da suka rabu, ‘yan’uwan babanta suka hana saboda matsalar da suka hango daga wurin dan China.

Ta ce tana tsohon mijinta ya taba ganin kamar suna waya da dan China lokacin da take a matsayin matarsa har ya yi zaton suna tare ne.

Ita ma kanuwarta Asiya ta tabbatar wa majiyarmu Leadership Hausa cewa a iya sanita ba ta san ‘yar’uwata da wasu munanan dabi’u ba. Asiya ta bayyana cewa abin da suka yarda kawai kaddara ce kuma kowa da irin tasa.

Da aka tambayeta shin ko tsawon wani lokaci alakar soyayya tasu ta dauka?

Sai ta amsa da cewa bai wuce shekaru biyu ba.

Da aka tambayi Asiya cewar ta ganin ko ‘yan’uwarta a wasu lokuta kan amsa gayyatar saurayin nata domin raka shi unguwa?
Nan ma cewa ta ce ba ta taba jin haka ba.
Lokacin da aka tambaye ta idan haka ne ta ya ya har shi wannan dan China ya san gidan da Ummulkhutum take har takai shi ga zirga-birga?
Sai ta amsa da cewa kasan lamarin rayuwa kila ya jima yana bin diddiginta, kuma kila ya yi ta tambayar jama’a har ya gano gidan namu.
A karshe ta bayyana cewa mahaifiyarsu ta shiga mawuyacin hali, amma dai ta ce yanzu jikin nata da sauki.
Kungiyar ‘yan China masu kasuwanci a Nijeriya, (CBCAN), reshen Jihar Kano, karkashin jagorancin wakilin mutanen China, Mike Zhang, ta yi Allah-wadai da kisan Ummulkulthum Buhari (Ummita) da dan kasar China, Geng Kuanrong ya yi.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a madadin wakili mataimakinsa Guang Lei, Zhang ya ce kungiyar ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai cewa wannan laifi ne da ya kamata hukumomin tsaro da abin ya shafa su kula da shi cikin kwarewa kuma su hukunta wanda ya yi idan har an kama shi da laifi.

A cewar sanarwar, “Al’ummar ‘yan China mazauna Kano suna goyon bayan doka da oda yadda ya kamata”.
Har ila yau, al’ummar sun yaba da irin tarba da zama lafiya da aka yi wa ‘yan’uwa na kasar Sin mazauna Kano, inda suka yi alkawarin ci gaba da kasancewa bisa bin doka da oda, da sada zumunci da ba da gudummawa ga ci gaban Kano.

Daga nan, Mista Zhang ya jajanta wa iyalan marigayiyar.

A yayin da ake zaman makoki da alhinin abin da ya faru da Ummita, sai dai wani babban abin damuwa bayan takaicin kisan, wasu bata-gari masu matacciyar zuciya marasa tsoron Allah suka sace kayayyakin margayiyar a lokacin da suka je kai mata dauki.

Wani dan jarida a Kano, Abdullahi El-bash ya shaida cewa “An kwashe wa Ummita manyan wayoyinta da sarkokinta na alfarma gami da zobunanta na hannu da sauran kayayyakinta na amfanin yau da kullum bayan tururuwar kai mata dauki da jama’a suka yi a dakin nata”

El-bash ya ci gaba da takaicin cewa, “Wannan abin takaici ne da bakin ciki gami da Allah-wadai wanda ke ci gaba da nuna cewa hakika akwai karancin imani a zukatan al’umma a yau. Lallai ya kamata jama’ar da ke da irin wannan gurbataccen tunani su sauya halayensu domin samar da gyaran al’umma.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin da ke Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cikakken bayanin magana ta tsawon mintuna 15 da suka yi da marigayiya Ummakulsum Buhari (Ummita) ta wayar tarho game da saurayinta, mako guda kafin rasuwarta.

Da yake bayyana abin da suka tattauna da marigayiyar a wani faifen bidiyo da ke nuni da cewa a daya daga cikin majalisin karatunsa, Daurawa ya ce ta kira shi ne domin neman shawara a kan mafita kan kudurinta na aurar dan China saboda mahaifanta sun hana ta aurensa.

“Na ce mata iyayenki su na da gaskiya saboda bai kamata mata ku rika auren wanda ake da kokwanto a kan asalinsa, ba” in ji shi.

Sai dai malamin ya ce ya ba ta shawarar ta gindaya wa masoyin nata sharudda biyar kafin su yi auren.
“Sharadi na farko shi ne a tuntubi hukumar shige da fice ta kasa don tabbatar da ko da izini ya shigo kasar nan.

Na biyu, a yi bincike kan aikinsa a Nijeriya.

“Na uku, na san Sarkin Kano ya nada sarkin ‘yan China a Kano. Don haka a tambayi shugaban al’ummar kasar ta China ko sun san shi, yankin da ya fito da kuma abin da yake yi?

“Na hudu, ya kamata kuma a sanar da ofishin jakadancin cewa dan kasar China na shirin auren ‘yar Nijeriya. Na biyar kuma na umarce ta da ta sanar da Hisbah don ta kara koya masa addinin musulunci tun da ta ce min ya musulunta.

“Ummita ta kara da cewa iyayensa a kasar China sun amince da auren, amma iyayenta sun ki amincewa da auren.
“Amma na gaya mata idan kun cika wadannan sharudda guda biyar, zan shawo kan iyayenki su yarda ki aure shi,” in ji shi.

Daurawa ya kara da cewa addinin Musulunci ya amince da auren kabilu daban-daban, yana mai cewa addinin ya kyamaci nuna wariyar launin fata.

Da yake zantawa da majiyarmu Leadership Hausa, Sheikh Daurawa ya ce mafi yawancin auren da ake yi kasho 90 duk akwaki kwadayi a cikinsa. Ya ce wannan ba sabon abu ba ne a Nijeriya, domin ita ma ce tana sha’awar kudi da samartaka a duniya.
Sai dai ya ce ba zai iya magana a kan tarbiyar yarinyar ba, saboda Magana tana hannun kumuma domin kar ya fadi abin da ban san shi ba.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Koyawa ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Kano ranar Asabar da ta Gabata. Kiyawa ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 10 na daren Juma’a.

A cewarsa, Genga Kwaron wanda mazaunin unguwar masu hannu da shuni ce ta Nasarawa da ke Kano. Kakakin rundunar ‘yansandan ya ce wanda ake zargin saurayin marigayiyar ne, ya ce sun samu sabani ne wanda daga nan ne kuma ya farmaketa da wuka.

“Da yammacin muka samu rahoton da ke cewa wani dan Kasar China mai Suna Geng Kwaron, dan Shekara 47 mazaunin Unguwar Nasarawa a Kano ya je gidan budurwarsa mai suna Ummulkhultum Sani, ‘yar Shekara 22 da ke Janbulo a Kano.

“Samun labarin ke da wuya sai kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano, Abubakar Lawal ya tura jami’an ‘yansandan wurin da lamarin ya faru, inda aka garzaya da matar asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

“Nan da Nan aka damke wanda ake zargin, sannan aka mayar da lamarin sashin binciken manyan laifuka na shelkwatar rundunar ‘yansanda da ke Kano, domin ci gaba da bincike.

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce shari’a za ta yi aiki a kan dan kasar Sin din da ya kashe budurwarsa.

Ganduje ya bayyana hakan ne yayin taron kaddamar da shugabannin hukumomin gudanarwar Hisba da zakka da Hubusi da hukumar kula da al’amuran shari’a a fadar Gwamnatin Kano.

Ganduje ya ce maganar zubar da jini dole shari’a ta shigo. Ya ce tuni an ba da umarnin tsare dan kasar Sin din kuma za a hukuntashi yadda ya kamata.she

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *