• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Aisha Najamu Izzar So Tayi Kuka Da Zubar Hawaye Akan Sabon Zargi Da Ake Mata

ByLucky Murakami

Nov 4, 2022

Ficacciyar Jarumar shirin nan mai dogon zango Izzar so wanda Tashar Bakori Tv dake kan manhajar Youtube take kawo muku a duk sati wato Aisha Najamu wacce a cikin shirin ake kiran ra da Hajiya Nafisa.

Ta bayyana a cikin wata bidiyo data wallafa a dandalin TikTok inda take kuka tana zubda hawaye wanda hakan abin a tausaya mata ne, inda take fadin cewa a ina aka taba ganin tana iskanci ko zina da za’a ce suna iskanci.

Hakan ya biyo baya ne lokacin da wani matashi ya yi musu kudin goro a dandalin TikTok, dama haka rayuwa take laifin da wani ya aikata sai kaga ya shafi wani amma abin da Aisha Najamu tayi yana nuna cewa ta fito ne domin ta wanke kan ta kan abin da ake zargin su da aikatawa.

A cikin bidiyon da zaku kalla zaku ga yadda Aisha Najamu take kuma tana fadin cewa, su sana’a suke amma ba ana kiran su da karuwai ba.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *