• Mon. Jun 17th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Akwai Babbar Matsala: Rikicin Ali Nuhu Da Hannatu Bashi Ya Dauki Sabon Salo

ByLucky Murakami

Oct 25, 2022

Kotun Majistare ta 54 da ke Nomanslan a birnin Kano a karkashin jagorancin Mai shari’a Aminu Gabari ta nemi jarumar finafinan Hausa da aka fi sani da Kannywood, Hannatu Bashir ta bayyana a gabanta a zama na gaba ba tare da ta turo lauyanta don wakiltarta ba.

Tun farko jarumi Ali Nuhu ne ya yi karar jarumar bisa zargin cin mutuncinsa ta waya sakamakon rashin halartar daukar wani fim dinta da ya yi.

Tun a baya da take zantawa da manema labarai, Hannatu Bashir ta ce ta gayyaci Ali Nuhu don fitowa a wani fim din da ta shirya inda suka yi yarjejeniyar za a dauki fim din a ranar 10 ga Oktoba.

Sai dai Ali Nuhu bai halarci wurin daukar fim din ba lamarin da ya fusata jaruma Hannatu ta aika masa da sakon tes wanda shi ma ya aike mata da amsa.

“Abin da ya bata min rai a wannan magana shi ne da kansa Alin ya zabi wannan ranar da muka yi za a dauki fim din, amma bai zo ba kamar yadda ya yi alkawari haka kuma bai bayar da wani uzuri na yin hakan ba.

Sai na aika masa da sakon tes wanda a fahimtata ban yi amfani da kalmomi masu zafi ba. Shi ma ya aika min da amsa wanda ya yi min zafafan kalamai, amma ganin cewa shi babba ne sai na hakura ban sake aika masa da wata mummunar magana ba.”

A cewar Hannatu ita ya dace ta yi karar Ali Nuhu ba shi ya yi kararta ba.

A cewar Hannatu duk da cewa ba su yi yarjejeniya a rubuce ba amma shi kansa Ali Nuhu ba zai musanta hakan ba.

Aminiya ta ga wasu daga cikin sakonnin, inda a ciki Ali Nuhu yake cewa ba wai sun yi wata yarjejeniya ba ce a rubuce, don haka bai kamata ta turo masa sakonnin da ta tura masa da maganganun da cewarsa zafafa ne ba.

A hoton da ake zargi na sakon ne da Aminiya ta gani, an ga Hannatu na cewa Ali Nuhu bai yi mata adalci ba domin a cewartsa tun watan jiya ta so ta yi aikinta, amma daraktan shirin, wanda shi kuma na hannun damar Ali Nuhu ne, Sheikh Isa Alolo ya ce mata Alin yana aiki, a bari sai ya gama.

Ta kuma fada a cikin sakon cewa Alolo ya fada mata cewa Ali Nuhu ya ce 10 ga wata (Oktoba) za a yi, sannan ana gobe za a fara aikin ta ce ta kara magana, domin a cewarta idan ba a fara aikin ba a ranar akwai matsala.

A karshe ta ce, “Ba matsala na hakura, kuma insha Allah fim ko kyauta za ka yi min, ba zan sake sa ka ba in Allah Ya yarda.”

A wani martani da ake yadawa cewa Ali Nuhu ya mayar, wani hoton da Aminiya ta gani yana cewa ne, “Me na yi miki da za ki turo min irin wannan sakon?

Ali Nuhu ya kara da cewa zai dauki matakin hukuma, inda a cewarsa za ta yi bayanin kudin da ta biya shi, ko yarjejeniya da suka yi da ya saba.

A game da hakan, jaruma Hannatu Bashir ta ce lallai ba su yi rubutu ba, amma a cewarta, “Gaskiya kamar yadda muka saba mun yi magana ne kawai a waya babu wani rubutu da muka yi.

Kasancewar muna ganin mun zama daya ba mu yin abubuwanmu a rubuce.

Amma duk da haka shi kansa Ali ba zai musanta wannan yarjejeniya da muka yi ba.”

Sai dai a ranar Talata Hannatu ba ta samu damar halartar zaman kotun ba, sai dai lauyanta hakan ya sa Alkalin Kotun Mai shari’a Aminu Gabari ya nemi ta bayyana gaban kotun inda kuma ya dage zaman shari’ar zuwa ranar 25 ga Oktoba, 2022.

Aminiya ta leka shafin Instagram na Hannatu Bashir, inda ta gano cewa jarumar tana can Jihar Gombe, inda ake daukar wakar Dauda Kahutu Rarara ta Jagaba Shi ne Gaba.

Sai dai a wani lamari mai cike da ban-mamaki, an gano hoton jarumar tare da Forudusa Abubakar Bashir Maishadda suna zaune, inda a kasan hoton ya rubuta cewa, “Cif El-Mu’az ga ni ga mutuniyar muna jiranka a Gombe.”

Hannatu Bashir dai mutuniyar El-Mu’az Birniwa ne, sai dai shi kuma Maishadda babban na hannun damar Ali Nuhu ne, wanda ya ba wasu mamaki ganin ya sa hoton jarumar tare da shi suna murmushi a daidai lokacin da take kotu da Ali Nuhu.

An dai dade ba a ga Maishadda da Ali Nuhu ba, musamman a wajen wakokin Rarara da a da can Ali Nuhu yake bayar da umarni.

Shin ko dai su ma sun samu sabani ne sun raba gari? Wannan dai lokaci ne zai bayyana.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *