An gano baiwar Allah da aka tsinci gawanta a ruwa wanda da farko ba’a san daga inda ta fado ba a har aka same ta a wani yanki.
Lokacin da aka tsincetan dai kusan duk ta canja kamannnin ta kuma ba’a san daga inda ta fito ba.
Sai dai wakilan mu sun tabbatar mana da cewa yarinyar dai an samu gidan su, tana unguwar state Low cost Block F12 ne a cikin Bauchi babban birnin jahar.
Ta gamu da ajalinta ne a mashigan State lowcost daura da Multipurpose a garin Bauchin ruwan ya tafi da Ita. Inda anan akaita binciken inda za’a sameta ba’a san inda ta tafi ba.
Cikin ikon Allah a wani yanki na kusa inda ba’a san yarinyar ba a nan aka sameta kafin a gane gaskiyar inda ta fito
Muna rokon Allah yajikanta ya kuma kyautata namu bayan nata.