A Safiyar Jiya Asabar ne aka fara yaɗa waɗansu hotuna a aoshiyal midiya na Tsohuwar jarumar Kannywood Fati Baffa Fagge wacce akafi sani da fati (Bararoji) waɗanda suka nuna yadda jarumar ta rame matuka.
Ganin hotunan ne yasa mutane suka dinga surutu kan cewa kodai tsohuwar jarumar tayi rashin lafiya ne? Idan haka ne kuma, wace irin cuta ce take damun ta?
Binciken mujallar Fim ya nuna cewa asali dai hotunan sun fara bayyana ne a shafin jarumar na TikTok daga nan suka yaɗu izuwa sauran wasu shafukan na soshiyal midiya. Mujallar Fim ta kira jarumar a waya domin tabbatar da halin da take ciki.
Mun tambaye ta ko tana da masaniya kan surutun daya ɓarke game da ita a soshiyal midiya.