Wani mutum mai suna King Principal ya bayyana karamcin da wasu mabarata da ya taba taimako suka masa.
Principal ya bayyana cewa ya saba bawa yaran kyautan kudi duk lokacin da suka taho wurinsa suna bara.
Amma, a wata rana, Prince ya ce yunwa ta kama shi kuma ya sanar da yaran halin da ya ke ciki.
Ba tare da bata lokaci ba, suka tattara kansu suka masa karo-karon kudi suka mika masa.
Prince ya karbi kudin da murmushi a fuskansa, ya kirga ya gano N280 suka tara masa.
Prince ya dubi yaran cike da mamaki a fuskarsa ya musu godiya kwarai da gaske.
Amma daga bisani ya canja ra’ayinsa ya mayar musu da kudin.