Bayan daura auren wata matashiyar budurwa mai suna Hauwa Abdullahi Shehu wacce aka fi sanin ta da Ummi, tare da Angon nata mai suna ASP Abdulmuhyi Bagel Garba a ranar Asabat biyar 5 ga wannan watan da muke ciki na Fabrairu, sai Allah ya karbi ran Amaryar mai suna Hauwa Abdullahi Shehu.
Kamar yadda shafin mr_mrs arewa dake kan dandalin sada zumunta na instagram ya wallafa hoton Amaryar tare da Angon nata, da kuma labarin mutuwar Amaryar Hauwa Abdullahi Shehu kamar haka.
Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun: Feb 5th Dan Allah ku karbi wannan a matsayin jan hankali don yiwa Ummi addu’a. Allahumma gafirlaha warhamha waafiha wa’afu’anha” Allah ya yafe mata kura kuranta sannan ya bata jannah.
Sannan kuma suka wallafa hoton Ango da Amaryar kamar yadda zaku gani a kasa.
https://www.instagram.com/mr_mrs_arewa/?utm_source=ig_embed&ig_rid=e8fe5aa1-01a7-441a-8af9-3a09933cd829
Bayan wallafar rasuwar Amaryar mai suna Hauwa Abdullahi Shehu mabiyan shafin sun yiwa mata addu’ar Allah ya gafar ta mata, ya yafe mata dukkan wani kura-kuran ta.