Kamar yadda kuka sani abubuwa da dama suna faruwa akan wannan matashiyar yarinya Safa wanda a yan kwanakin nan mutane suke ta nuna rashin jin dadinsu akan irin hakayen da take nunawa.
Fitacciyar mawakiyar Arewa kuma Jarumar Arewa Safa wadda aka fi sani da Safara’u kwana cassain ta fara zanen ta na farko a jikinta, jarumar ta dauki hotonta a dandalin sada zumunta inda ta nuna farin cikinta a lokacin tana mai cewa “Y’all, I did my first tattoo, Alhamdulillah”
Ko da yake wasu daga cikin masu amfani ba sa samun shi musamman a Twitter idan wasu masu amfani da su suna yin sharhi suna ba ta shawara da ta yi watsi da yammacin turanci kuma ta kasance kamar musulmi da bahaushiya.
Bayan faruwar wannan abu da kuma sauran abubuwa marasa dadi da suke faruwa akan wannan yarinya Safa hakan yasa wata uwa ta gari tayi magana.
[ads1]
Cikin wani bidiyo ta bayyana me tsawon minti uku da wasu dakika hajiyar tayi kira ga su mazan da suke tare da Safa a wajensu da suji tsoron Allah kuma su duba shin zasu iya yima kannensu abinda da suka yima wannan yarinya.
“Ace kuna maza zaku dauke yarinya karama wanda nasan nakai matsayin uwa a garinta ku kebe da ita kuna koya mata wasu abubuwa marasa kan gado”
Sannan tayi ga ita Safa da kuma mahaifiyarta ta da suji tsoron Allah akan wannan lamanin dake faruwa saboda sam bai dace ga yarinya yar musulma kamarta ba.
Ga cikakken bidiyon da hajiyar ta sake zaku iya kallonsa:
Muna rokon Allah ubangiji ya shirya mana zuri’a, ya kuma sa mu gama da duniya lafiya.
[…] Idan baku manta ba shafin amihad.com a baya ya kawo muku yadda Wata Uwa Ta Gari Ta Yiwa Safa Safara’u Nasiha Akan Abinda Take. […]