• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Allah Sarki! Yadda Wata Budurwa Ta Mutu Ana Dab Da Aurenta

ByLucky Murakami

Aug 2, 2022

Innalillahi Wainna Ilaihi rajiun: Allah Ya Karbi Rayuwar Wata Amarya Mai Suna Rukayya Ibrahim Allah Sarki.

Wata Budurwa Mai Suna Rukayya Ibrahim Ta Rasu Ana Gaf da Auren Ta Allah Sarki Wannan Lamari Yayi Matukar Gir’giza Alumma Inda Jama’a Suka’ji Wannan Mutuwar.

An Samu Wannan Labari Ne Daga Wajen Saurayin da Zai Aure Ta Mai Suna” Safiyanu Abubakar Inda Ya Fadi Mutuwar Tata Cikin Tashin Hankali.

Allah Sarki Muna Fatan Allah Uban’giji Subhanahu Wata Ala Yajikan Wannan Amarya Da Rahama Kuma Allah Yasa Aljanna Ce Makomar ta.

Wannan Kenan kadan Daga Rahoton Mu Akan Wannan Rashin da Akai Na Wannan Baiwar Allah data Ke Shirin Zama Amarya Allah Yajikan ta da Rahama.

Yan uwa kudan bawa kanku minti kadan ku karanta matsalolin dake kawo rabuwar aure a kasar hausa, saboda hakika mace-macen aure yana daga cikin manyan matsaloli da muke fama dasu a wannan lokaci.

A yayinda wasu basu da burin daya wuce suyi auren don rayar sunnanr fiyayyen halitta, amma sai kaga anayin auren matsaloli sun kunno kai.

Shin menene yake kawo yawan mutuwar aure a kasar hausa?

Akwai abubuwa masu yawan gaske wadanda suke jawo sanadiyar mutuwar aure. Kadan daga cikinsu, suna abkuwa ne tun kafin ayi auren, wadansu kuwa suna faruwa bayan ma’auratan suna zaune tare.

Wadanda suke abkuwa kafin auren sun hada da rashin sanin ilmin aure, soyayyar karya da son abin duniya. A lokuta da dama soyayyar karya na gudana tsakanin namiji da mace, a inda daya daga cikinsu, baya son guda, amma sai yake/take nuna soyayyar karya.

A irin wannan yana yin idan anyi auren, to ba zai dauki lokaci mai tsawo ba zai mutu, saboda tun farko an daura shine a bias sigar karya.

Abu na uku da yake haddasa mutuwar aure, tun ma kafin ayi auren shine yawan son abin duniya daga mazan da matan. Misali sai kaga namiji yana furtawa wai shi ba zai auri yarinya ‘yar gidan Malam Shehu ba, (watau talaka).

Shi yafi son ya auri ‘yar gidan attajiri (watau mai kudi) wanda zai basu gida su zauna, da mota da kuma gwaggwabar gara, wacce zasu dade suna amfani da ita.

Daga bangaren matan kuma, suma akwai wadanda mai abun hannun (kudi) kawai suke so su aura. A inda zaka ji suna cewa su sai hadadden gaye kawai zasu aura. Watau wanda yake ta tabkeken gida, da manyan motoci da kudi a makare a banki.

Daga karshe ga jerin manyan dalilai guda 10 daya kamata ku sani
  1. Rashin sanin daraja da hakkokin aure
  2. Kaucewa koyarwar Manzon Allah game da zamantakewar ma’aurata
  3. Girman kai ga maza, rashin kunya ga mata
  4. Yin aure saboda kawai don sha’awa, dukiya ko wani son abin duniya
  5. Karin aure yayin da babu ikon yi
  6. Rashin adalci da wulakanta abokin zama
  7. Rashin bin ka’idojin saki
  8. Jahilci
  9. Rashin son haihuwa
  10. Baiwa al’adu muhimmanci fiye da addini
Ina Mafita Ga Wannan Matsaloli?

Hanyoyin da za’abi ayi maganin yawan mutuwar aure a kasar Hausa sun hada da; gina aure a doron soyayyar gaskiya, rage son abin duniya, sanin ilimin auren kafin ayi shi. Sauran sun hada da iyaye su koyawa ‘ya’yansu mata tsafta, girki da ladabi da biyayya kafin aurar dasu.

Mazaje su rinka ba wa matayensu kulawa ta musamman, da kuma yaba masu idan sunyi girki mai dadi ko kuma kwalliyar data burgesu. Sannan su kuma yi kokari suna zama tare da iyalensu a cikin gida. Har ila yau su daina amfani da wayarsu idan suna tare da iyalensu, sai dai idan kiransu akai a wayar to sai su amsa”.

Ya kamata sarakuna da malamai su yi wani abu wanda zai taka rawa wajen binne duk wasu al’adun da ba su dace ba, saboda idan aka yi tunani suna haifar da raini maimakon kawo ci gaban al’umma.

Ba kuma wani lokacin da ya fi dacewa a daukin matakin da yafi dacewa kamar yanzu, a koma kan hanyoyin da suka dace, wadanda kuma me Alkur’ani ya ce, ko kuma Hadisin manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce, ba wai maganar wata al’adar da ba ta zama dole ba.

Me karatu, a ganinka baya ga abubuwan da aka zayyana a sama, wadanne abubuwa ne ke haddasa yawan mutuwar aure a kasar Hausa ? Kuma ina mafita?.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *