Bayan dogon hutu da aka tafi bayan kammala shirin Labarina series season 4, a wannan karon shirin ya dawo da wani sabon salo wanda yake dauke da sabbin jarumai.
A kwanakin baya dai duniya ta samu labarin matsalolin da daraktan shirin Mallam Aminu Saira ya samu da wasu jaruman shirin wanda hakan ya jawo janyewar jaruman daga aiki a cikin shirin
Kamar yadda muka sani Jaruma Nafisa Abullahi na daya cikin manyan jaruman da tauraruwarsu ta haska a cikin wannan shiri me dogon zango na Labarana
Bayan wasu matsaloli da jarumar ta samu da masu shirya shirin hakan ya sa jarumar ta fidda sanarwar janyewarta daga aiki a cikin wannan shirin wanda hakan ya jawo cece kuce akan jarumar da zata iya maye gurbin Nafisa Abdullahi a cikin wannan shiri.
Mutane da dama cikin shafukan sada zumunta sunyi ta bada ra’ayoyinsu akan jarumar da zata iya maye gurbin jarumar a cikin shirin, wanda a gefe guda kuma wasu mutanen suna cewa babu wata jaruma da zata iya maye gurbin tayi aiki kamar yadda ita jaruma Nafisa Abdullahi ta taka rawa a baya.
Sai dai cikin kwanakin nan daraktan shirin Mallam Aminu Saira yaci gaba da daukar shirin Labarina series season 5 wanda wasu daga cikin jaruman shirin suka bayyana jaruma Fati Washa a matsayin wanda zata maye gurbin Nafisa a cikin shirin.
Sannan kuma anga bidiyon Jaruma Fati Washa a wajen daukar ci gaban shirin kamar yadda zaku gani a bidiyon dake kasa: