Duniya ina zaki damu ‘Yan sanda sun cafke wani a yayin da ya ke yunkurin binne mahaifiyar sa akan rikicin fili da ya shiga tsakanin su a kasar Kenya.
Mazauna a kauyen Siuno wanda ke mazabar Kabuchai suka ceto idan wannan tsohuwar matar a yayin da ta yi ihu suka ji daidai lokacin da dan na ta mai suna Chris Wamalwa ke kokarin binne ta a bayan gidan su a ranar Alhamis 19 ga watan Agusta.
Kafafen yada labarai na Daily Nation ta ruwaito cewa Wamalwa ya fusata da mahaifiyan na sa Beatrice Nasaka, bayan ta siyar da wani filin ta da ya ke sa ran zai gada a hannun ta. A yayin da suke magana akan filin tare da ita ya yanke hukunci zai binne ta da ran ta.
A lokacin da mahaifiyar Chris ke bada na ta bayanin game da lamarin a asibitin Bungoma County Referral Hospital bayan a ceto ta, ta bayyana cewa dan ta ya so ya binne ta ne a bisa dalilin kin bashi wani kaso daga kudin da aka siye filin bayan da siyar da filin.
“Ni bazawara ce sannan kuma abubuwa da mallaka su ne za su cece daga shiga cikin talauci. Na siyar da wannan filin nawa don nayi amfani da wannan kudin wa kai na amma da dan nawa ya jin labarin na siyar da filin, tuni ya taso ya zo gida a guje ya ce na ba shi na shi kason. Ya so ya binne ne bayan na ke ba shi abunda ya ke so,” haka Beatrice ta ce.
A yanzu haka Chris dan shekara 40 na hannun ‘yan sanda.