Labarin da muke samu a yau shine rundunar ‘yan sandan jihar Gombe sun gabatar da kama wani mutum da ake zargi da yi wa wata yarinya mai shekara 16 fyade a makabarta a karamar hukumar Kaltungo da ke jihar Gombe.
Kamar yadda majiyar amihad.com ta tabbar batun hakan na dauke ne a wata takarda mai dauke da sanya hannun Kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar a madadin Kwamishinan ‘yan sandan jihar ne Ishola Babatunde Babaita.
Ya ce magidancin mai suna Reuben Azariah na makwabtaka ne da yarinyar da ake zargin ya yi wa fyaden.
ASP Mahid, ya ce jami’an ‘yan sanda a karamar hukumar Kaltungo sun samu rahoton hakan ta wajen wata mai suna Abigail Yunusa, mahaifiyar yarinyar da aka yi wa fyaden.
Majiyarmu jaridar Aminiya ta rawaito cewan ASP Mahid ya ce a ranar biyu ga watan Satumbar 2022 da misalin karfe 8:30 na dare ne ita Abigail Yunusa da ke zaune a unguwar Tarmana a karamar hukumar ta Kaltungo ta kai musu rahoton shi wanda ake zargin Reuben Azariah da suke zaune da shi a unguwa daya kan cewa ya yiwa ‘Yar ta da aka (sakaye sunanta) mai kimanin shekara 16 fyade da karfin tsiya a kan wani kabari da ke harabar gidan da suke a nan unguwar Tarmana.
A cewarsa, daga karbar rahoton ‘yan sanda suka shiga neman sa inda suka yi nasarar kamo shi Reuben, aka kuma dauke shi da yarinyar duka aka kai su babban asibitin garin kaltungo domin a duba lafiyarsu.
Daga nan ya ce da zarar sun kammala bincikensu na ‘yan sanda za su tura shi wanda ake zargin zuwa kotu.
Har ila yau a wani labari mai kama da wannan Jami’in hulda da jama’ar yace yan sanda sun kama wani mai shekaru 55 a Gombe mai suna Musa Umar da shi ma ya yiwa yar shekara 6 fyade a wani kango da ba’a kammala ba a unguwar Kagarawal.
ASP Mahid Mu’azu ya ce ‘yan sanda sun samu korafi ne daga wani mazaunin unguwar Alhaji Musa Shehu, na shi Musa Umar mai shekara 55 da ke zaune a unguwar ta Kagarawal, inda ya yaudari wata yarinya mai shekara shida ya dauke ta zuwa wani kango ya yi mata fyade.
Daga nan ya ce suna karbar korafin suka tsunduma nemansa suka kuma kamo shi, da shi da yarinyar sun kai su asibiti dan duba lafiyarta, shi kuma daga bisani za su tura shi zuwa kotu.