Wani bature dan Ingila ya bayyana yadda ya gano wayarsa a Najeriya bayan wata guda kacal da ta yi batar dabo.
Baturen mai suna, Darren, ya bayyana afkuwar wannan lamari ne a shafinsa a Twitter.
Cikin mamaki mutumin ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan wata daya da batan wayarsa a birnin Liverpool amma kuma da ya yi bincike ta manhajar iCloud sai ya gano cewa a halin yanzu wayar tana Jihar Edo a Najeriya.
Ya dai sanya bayanan da ya samo kai tsaye a shafinsa na Twitter domin ya shaida wa mutane inda wayar tasa take a wannan lokaci.
“Na rasa wayata wata daya ke nan yanzu a garin nan…, yanzu ina shiga iCloud dina sai nake ganin cewa wayar tawa ta tafi hutu Najeriya,” a cewar Darren.