Munyi karo da wani labari wanda wani ango ya fasa auren amaryarsa saboda garjartarta inda yace shi baya son auren gajeriyar mace doguwa yakeso.
Jaridar Aminya ta rawaito cewa wata budurwa ’yar kasar Tunisiya da take shirin zama amarya ta rika samun sakonnin tallafi daga sassan duniya bayan an yi watsi da bikin aurenta lokaci guda saboda sukar da surukarta ta yi mata cewa ba ta gamsu da yadda kamanninta yake ba.
A karshen watan jiya ne budurwar mai suna Lamia al-Labawi, ta wallafa labari mai ban-tausayi a shafin Facebook inda ta bayyana yadda abin da ya kamata ya zama mafi alheri a rayuwarta ya koma wani mafarki mai ban tsoro.
Ya kamata a ce an yi aurenta da angonta shekara hudu da suka wuce amma sai yanzu; an shirya komai kuma sun kashe makudan kudi don ganin komai ya tafi yadda aka tsara, amma abin da ba su yi la’akari da shi ba, shi ne furucin mahaifiyar ango.
Lamia ta ce, ba ta taba haduwa da mahaifiyar angonta ba, kuma maimakon a yi mata tarba cikin mutunci zuwa cikin danginsu, abin da ta samu a ranar aurenta shi ne munanan kalamai.
Bayan fara bikin daurin auren, baki sun hallara, surukar Lamia da wasu sun kudiri wani abu a zuciyarsu.
A gaban kowa, surukar ta matso kusa da danta (angon) ta ba shi umarnin ya soke bikin auren, tana mai cewa amaryar “gajera ce kuma mummuna” da ba ta cancanci ta auri danta ba.
A baya hotunan Lamia ne kawai ta gani, kuma da alama ta ji takaici sosai bayan ganin amaryar ido da ido.
Cin mutuncin da uwar angon ta yi wa amaryar bai zama wani babban al’amari ba, sai dai bakin sun yi mamakin abin da angon ya yi.
Ya bi umarnin mahaifiyarsa, kuma duk rokon da mutane da yawa suka yi a wurin bikin, amma ya watsar da auran Lamia ya bar harabar bikin tare da mahaifiyarsa.
Nan da nan labarin ya bazu a shafukan sada zumunta, kuma Lamia al-Labawi ta fara samun sakonnin goyon baya daga mutanen da suke gaya mata cewa, ta dage ta kuma gane cewa angon bai cancanci yin aure ba.
“Tare da soyayya da ’yan uwantaka, ina gaya muku, ku daga kanku ku fuskanci duniya da dukkan karfinku,” Dan wasan kwaikwayo na Tunisiya, Hedi Al-Mejri, ya rubuta wa Lamia.
“Ba ki rasa miji ba. Kin rasa wani abu da zai iya zama la’ana a rayuwarki. Kina iya samun ’yanci marar musanya. Kada ki karaya, kada ki ce ke marainiya ce.
“Duniya tana dauke da darasi, kuma dole ne mutum ya bambance tsakanin miji da sauran maza. Ubangijina zai saka mata da alheri, insha Allahu za ta samu abu mai kyau a gaba.
“Auren Lamia darasi ne daga darussan rayuwa, kuma gaba ta fi kyau, insha Allahu,” wani mai suna Sana Cherif ya rubuta a Facebook.
Lamia al-Labawi ta fitar da wani faifan bidiyo tana gode wa kowa kan kalaman karfafa gwiwa da suka aike mata. Abin da za a iya cewa game da angon shi ne, akalla bai yi watsi da auren a kashin kansa ba.