AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Home » Ana Shirin Ninka Kudin Kiran Waya Dana Data A Nigeria
    News

    Ana Shirin Ninka Kudin Kiran Waya Dana Data A Nigeria

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 9, 2022No Comments2 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Pinterest Email

    Za a ninka kudin kiran waya da sayen data a Najeriya karkashin tsarin Gwamnatin Tarayya na kara harajin amfani da waya a kasar.

    Idan aka aiwatar da karin, ’yan Najeriya za su rika biyan N40 a kan kiran minti daya, maimakon kimanin N20; farashin data kuma zai iya kaiwa N2,500 a kan kowane gigabyte.

    Bincikenmu ya gano cewa a kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin aiwatar da karin harajin kaso 5 cikin 100 a kan harkokin sadarwa, wanda hakan zai kara yawan harajin da ake biya a harkokin sadarwa zuwa kashi 12.5 cikin dari.

    Masana a bangaren sadarwa sun ce sabon tsarin harajin, baya ga shafar masu amfani da waya ba ne kawai, zai kuma kara nauyin haraji a kan kamfanonin sadarwa wanda a karshe zai haifar da tsadar harkokin sadarwa.

    Ministar Kudi da Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta bayyana shirin ne a taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da haraji kan ayyukan sadarwa a Najeriya wanda Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta shirya.

    Ta bayyana cewa harajin kashi 5 cikin 100 din yana cikin dokar kudi ta 2020.

    Ta ce za a rika fitar da kudaden harajin da aka tara a kowane wata, ko kafin ranar 21 ga wata.

    Matakin a cewarta, wani bangare ne na kokarin da Gwamnatin Tarayya na bunkasa kudaden shigar da ba na mai ba, sakamakon raguwar kudaden shiga, musamman daga bangaren mai.

    Sai dai shawarar ta fuskanci suka daga Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Isa Ali Pantami.

    Yayin da ma’aikatar kudi ta bayyana amincewar da shugaban kasa na aiwatar da sabon harajin kan harkokin sadarwa, kamar yadda dokar kudi ta tanada, ma’aikatar Pantami ta yi kakkausar suka kan cewa sabon harajin zai yi illa ga bangaren da masu amfani da wayoyi.

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email

    Related Posts

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022

    Yadda Aka Kama Malamin Addini Yana Lalata Da Yan Mata Biyu Yan Uwan Juna

    November 23, 2022
    Add A Comment

    Leave A Reply Cancel Reply

    Check Also

    Ya Kamata Kusan Da Wadannan Tsaruka Na Tallafi Da Ake Bawa Yan Nigeria

    January 27, 2023

    FG Begins SMEDAN ₦1.5m Loan – Application Portal

    January 20, 2023

    How to Obtain an Ecowas ePassport as a Holder of a Nigerian Passport

    January 20, 2023

    Easy Way to Apply for a Visa in Nigeria

    January 20, 2023

    Apply 2023 Microfinance Bank Kaduna Recruitment

    January 20, 2023
    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2023 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.