Shiekh Isa Taliyawa ya gargadi mata da cewa kar su sake zuwa Sallah a masallacin Juma’a na Bolari, domin kungiyar Izala ta hana cudanya tsakanin maza da mata, amma yanzu sai ga mata na zuwa Sallah a masallaci.
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa na kungiyar Izala, reshen Kaduna, Sheikh Usman Isa Taliyawa, ya ce lalacewar shugabancin kungiyar ce ta sa mata ke zuwa masallaci.
“Mata su nemi duk inda za su je Sallah, amma banda Masallacin Bolari ” inji Taliyawa.
Malamin ya yi gargadin ne a wa’azinsa gabanin Sallar Idin Layya a Babban Massallacin Izala da ke unguwar Bolari a Jihar Gombe.
A cewarsa, “Sai ka ga mace ta yi lalle ko zane-zane a hannunta ta je masallaci; yin hakan ba daidai ba ne.
“Duk lalacewar Izala bai kamata a koma gidan jiya ba,” in ji shi.
Ya ce in banda lalacewar shugabancin Izala, babu dalilin da zai sa a bar mata suna zuwa masallaci a irin wannan yanayin.
Ya kara da cewa fitina ce ga mata zuwa masallaci domin tunda aka kafa kungiyar Izala ba ta yarda a hadu waje guda maza da mata ba.
Ya ba da misali da cewa tun daga kan malamai zuwa shugabanni da ’yan agaji babu wanda matarsa take zuwa masallaci.
“Mata masu zaman kansu ne kowacce ta fi karfin mijinta ko ma wacce ba ta san addini ba, su ne suke zuwa masallaci,” in ji Sheikh Taliyawa.