Duk da irin makudan kudade da ake ware wa bangaren ilimi a Nijeriya, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kashi 31 na ‘yan Nijeriaya ba su iya karatu da rubutu ba.
Karamin ministan ilimi, Rt Honourable Goodluck Opiah, shi ya bayyana hakan a wurin taron ma’aikatu kan ranar jahilai ta duniya ta 2022 tare da ganin an kawar da lamarin cikin sauki.
Ya ce a yanzu haka alkaluman 2022 sun nuna cewa akwai kashi 31 na jahilai a kasar nan, inda ya ce adadin ya ragu da na shekarar 2015 da aka samu kashi 38.
Ministan ya kara da cewa wannan rana da Majalisar Dinkin Duniya ta ware na tantance adadin marasa ilimi ya bayar da damar bunkasa harkokin ilimi tare da inganta fannin a ko’ina a fadin duniya.
Takaddama Kan Shirin Daukar Sabbin ‘Yansanda
A ranar 11 ga watan Oktoba 2020 mun yi sharhi a kan takaddamar da ke tsakanin Rundunar ‘Yansanda da Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda a kan shirin daukar sabbin ‘yansanda don fuskantar matsalolin tsaro a kasar nan.
A wannan karon Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda ta sanar da shirin fara daukar sabbin Kuratan sai Rundunar ‘Yansanda ta sana da cewa, al’umma su yi watsi da sanarwar.
Duk da Hukumar Kula da Aikin “Yansanda ta dakatar da shirin daukar Kuratan, amma hakan yana nuna cewa, har yanzu takaddamar da ke tsakanin Rundunar ‘Yansanda da Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda yana bai kare ba.
A kan haka mjka sake kawo muku sharkin da muka yi a waccan lokacin don gargadi a kan matsalar da takaddamar ka iya haifarwa ga bangaren tsaron kasar nan.
Yayin da ake fuskantar matsalar tsaro a sassan Nijeriya, wanda hakan ke haifar da kiraye-kirayen kara daukar matakin ganin an kawo karshen mastalolin gaba daya, amma sai gashi ‘yan Nijeriya sun wayi gari da takaddama a kan waye zai jagoranci daukar Kurata 1,000 aikin rundunar ‘yansandan Nijeriya.