• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Asiri Ya Tonu Gaskiyar Magana Akan Matan Da Sukafi Karfin Namiji Da Aure

ByLucky Murakami

Aug 2, 2022

Barka da zuwa wannan shafi me albarka, akwai wata tambaya da ta jawo muhawa a shafukan sada zumunta musamman shafin TikTok wanda amihad.com taci karo dashi akan shin ana samun matan da sukafi karfin namiji da aure.

Wannan abu dai kamar yanda bincikenmu ya tabbatar mana ya faru ne bayan mutuwar auren wata mata, inda ake cewa ita ba tsarar auren mijin data aura bace.

Kada na cikaku da surutu yanzu zamuyi duba cikin wannan lamari na abinda ya faru daya jawo cece-kuce.

Da gaske mace na fin karfin namiji da aure ?

Bayan mutuwar auren Nafisa Ishak ta haddasa muhawara wadda ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumta na zamani.

In baku manta ba Nafisa Ishak itace wannan yarinyar da tayiwa Mallam Aminu Daurawa rasar kunya wanda abun ya kaure shafukan sada zumunta na tsawon lokaci.

Sai dai bayan faruwar hakan ne auren ita wannan jarinya da ake cewa jaruma ce a masana’antar shirya fina finan hausa ya mutu. Hakan yasa mutane suke tunanin abinda tayiwa malam ne ya jawo mata wannan matsala ta mutuwar aure.

Hakan yasa wasu mutane suketa ta ji mata maganganu kala kala akan wannan abu.

Sai dai ta bakin Jarumar tace auran talaka bashi da wani amfani musamman ga yarinya yar dadi wacce bata saba da wahala kada ta sake batasha wahala a gidan iyayen taba taje gidan miji kuma tasha wahala.

Hakika wannan magana ta fusata mutane da yawa wanda suka nuna fushinsu akan hakan kamar yadda shafin amihad.com ya tabbtar.

Inda tace itafa zataci gaba da wayarwa da yan uwanta mata kai musamman masu kyau da kada su sake su auri wannan ba sa’ansuba wanda bazai iya basu duk wata kulawa ba musamman tajin dadin rayuwa.

Masu karatu wannan daliline yasa mutane suketa muhawara kamar yadda shafin tsakar gida ya tabbatar magana cikin bidiyon daya wallafa a shafin Youtube. Domin jin yadda ta kasance zaku iya kallon wannan bidiyon kamar yadda zamu gabatar muku dashi a kasa.

 

Bayan sauraran wannan jawabi nasa, me zaku iya cewa akan wannan muhawa. Muna jiran muji ra’ayoyinku.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *