• Fri. Mar 29th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Asirin Shugaban Makaranta Da Yayi Lalata Da Dalibai Mata 7 Ya Tonu

ByLucky Murakami

Sep 10, 2022
An Kama malamin addinini yana lalata

Rahoton da muke samu shine dambarwa ta biyo bayan zargin lalata da dalibai bakwai da ake yi wa Shugaban Kwalejin Musulunci ta Hassanat da ke Ilori a Jihar Kwara.

Kamar yadda binciken mu ya tabbatar wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa shugaban mai suna Samuel Prosper ya buya, tare da rokon a yafe masa.

To sai dai binciken majiyarmu jaridar Aminiya tayi ya nuna a ranar Alhamis gwamnati ta rufe makarantar, sai dai zanga-zangar shugabbaninta ya sanya Ma’aikatar Ilimi sake bude ta.

Wata ma’aikaciuya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce duk da shugaban da ake zargi ya ajiye aiki, makaranatar ba ta da dalibai masu sunyaen da kafafen yada labarai suka rawaito a makaranatar.

Ta kuma ce sunaye biyu ne kadai na dalban nasu, suma kuma sun karyata labarin.

Ta ce kafin wannan lokacin, shugaban makaranatar ya sha korafin ana yi wa rayuwarsa barazana, musamman kasancewarsa Kirista da ke jagorantar makaranatar Musulmi mai zaman kanta.

“Shi kuma shugaban riko ne, kasancewar tsohuwar shugabar ta samu wani aikin a Abuja.

“Da yake shi ne mataimakinta, sai aka ba shi kafin zabar wani sabon shugaban kuma ana tsaka da haka ne mai makarantar ya rasu,” in ji ta.

Wata makwabciyar makarantar, Misis Mojirayo, ta ce, “Ba mu taba jin wannan labarin ba sai yau da safe.”

Har ila yau, kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce babu wani dan jarida da ya tabbatar wa faruwar lamarin.

“Abin da na ce shi ne babu wanda ya shigar da korafi makamncin wannan ofishinmu,” in ji shi.

A nasa bangaren, kakain ma’aikatar ilimi ta jihar, Peter Amongbonjaye, ya ce ba shi da hurumin yin magana kan lamarin.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *