Wata mata ta bayyana yadda mahaifinta ya kwashe shekaru yana yi mata fyade ita da kannenta mata.
Matar mai suna Aziza Kabibi tace mahaifinta ya fara yi mata fyade da bugunta lokacin da take da shekara 12 a duniya, inda tace tayi fatan dama ba ta zo duniyar nan ba. Shafin LIB ya rahoto.
Mahaifiyarta ba tayi komai ba a kai
Ta bayyana cewa mahaifiyarta tana sane da abinda mahafin nata yake mata amma ba tayi komai ba akai.
An hana ta zuwa makaranta sannan an ware ta daga cikin ‘yan’uwan ta don kada ta gayawa kowa abinda ake yi mata.
Matar ta kuma bayyana cewa mahaifin nata ya gaya mata cewa lalatar da yake da ita “umurnin ubangiji ne”
Tace ta so ta gudu ta bar gida a wani lokaci amma sai ‘yan’uwanta maza da mata suka hana ta.
Ta bayyana cewa ta fahimci idan ta bar gida, mahaifinta zai fara lalata da kannenta mata don haka sai ta tsaya. Mahaifinta yayi mata alkawarin cewa idan ta daina korafi, ba zai taba kannenta ba, don haka sai tayi shiru.
Sai dai, daga baya ta gano cewa mahaifin nata yana yiwa kannenta mata fyade
Ta haifi yara biyar tare da mahaifinta
Tana shekara 15 a duniya, da samu cikin farko da dan mahaifinta.
Ta samu juna biyu tare da mahaifinta sau biyar sannan dukkanin yaran, wadanda su ma suke a matsayin kannenta, a gida mahaifinta ya amshi haihuwar su.