• Sat. Jun 22nd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Auren Jaruma Nafisa Abullahi Menene Gaskiyar Magana?

ByLucky Murakami

Aug 3, 2022

Barka da zuwa wannan rubutu akan maganar auran Nafisa Abdullahi shin dagaske ne, ko kuma jita jitar mutane ne?

Jaruma a masana’antar kannywood Nafisa Abdullahi anga wasu labarai akanta suna yawo cewa zatayi aure kuma abinma ya gabato ana maganar befi saura yan kwanaki ya rage a daura auren ba.

Amma sai dai maganar ce ba’a tabbatar ba shine akaji daga bakin jaruma shin dagaske maganar auranki inda tace itama kamar yadda aka maganar tana yawo agari itama haka ta gani, batada masaniya akan wannan al’amari.

Kazalika labarin dai labarin kanzan kuregena babu wannan maganar kwata kwata zancene kawai wani ya zauna ya kagoshi inda tace kowa yaji ya bar zance domin kagaggen zance ne.

Sannan jarumar tayi kira qa wa’yanda suke kirkiro irin wannan zance dasu guji sake kala mata irin wannan maganar ta aure alhalin ba ita ta sanar ba, tunda tasan lokacin aurenta baiyi ba.

Daman kuma hakan an saba yiwa yan matan kannywood rana daya kawai sai gari ya rude cewa wata jarumar zatayi labarai suyi ta yawo a shafukan sada zumunta, shiyasa wasu daga cikin jaruman koda auren zasuyi da gaske boyewa sukeyi ko kuma suqi bayyana ranar auren.

Daga karshe Nafisa Abdullahi dai ta nisanta kanta da wannan zance kuma ta ce inda auran nata yazo da kanta zata sanar ba wani ne daga gefe ba. Muna fatan kunji dadin wannan labari domin kallon cikakken bayani ku duba bidiyon dake kasa.

https://www.youtube.com/watch?v=g305tXyUFl8

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *