• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Ba Abinda Zai Hanani Inganta Rayuwar Alumma A Wannan Gwamnati – Sadiya Farouq

ByLucky Murakami

Jul 21, 2022

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa duk wani tugu da ‘yan baƙin ciki masu son ganin bayan kyawawan shirye-shiryen inganta rayuwa da gwamnatin Buhari ke yi domin cimma burin ‘yanto ‘yan Nijeriya marasa galihu miliyan 100 daga ƙuncin fatara zuwa shekara ta 2030 ba zai kashe mata ƙarfin gwiwa ba.

Ministar ta bayyana haka ne a martanin da ta yi kan wani rahoto da wasu masu kiran kan su ‘APC Initiative for Good Governance’, wato Ƙungiyar Tabbatar da Nagartaccen Mulki na APC, su ka bayar inda su ka yi iƙirarin wai ta kwashe dukkan Shirye-Shiryen Inganta Rayuwa da ma’aikatar ta ke aiwatarwa na dukkan jihohin ƙasar nan ta kai su Jihar Bauchi.

Ƙungiyar, wadda a Bauchi ta ke, ta yi iƙirarin ne a sanarwar da wani mai suna Nasiru Cigari ya rattaba wa hannu, inda ta ƙara da cewa wai ministar ta bar aikin ofishin ta ta tare a Bauchi domin ta taimaka wa mijin ta, Eya Mashal Abubakar Sadique (mai ritaya) wajen yaƙin neman zaɓen da ya ke yi na zama gwamnan jihar a zaɓen shekarar 2023 a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC.

A martanin da mai taimaka mata ta musamman a aikin jarida, Madam Nneka Ikem Anibeze, ta fitar, ministar ta bayyana cewa ita kan ta wannan ƙungiya, ƙungiyar ƙarya ce domin babu ita, sannan zargin da ta yi wani shiri ne na mugunta haɗi da ƙage.

A cewar ta, “Tun daga lokacin da aka kafa wannan ma’aikata a cikin watan Agusta na shekarar 2019, aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 20 ne su ka amfana da shirye-shirye daban-daban na ma’aikatar. Sun haɗa da matasan da su ka gama jami’a da ma waɗanda ba su gama ba su 1,064,774 waɗanda aka bai wa horo a ƙarƙashin shirin ‘N-Power’, waɗanda a cikin su Jihar Bauchi ta zama ta 11 daga cikin jihohi 36 da Gundumar Babban Birnin Tarayya.

Ta ce: “Jihohin da su ka fi amfana su ne Binuwai, Delta, Inugu, FCT, Kaduna, Kano, Legas, Osun, Oyo da Ribas, sannan sai Bauchi.

“A yanzu haka a ƙarƙashin shirin Ciyar Da ‘Yan Makaranta, jimillar yara miliyan 9.9 ‘yan aji 1 zuwa 3 a makarantun firamare na gwamnati 53,000 a duk faɗin ƙasar nan ana ba su abinci mai zafi sau ɗaya a duk ranar da su ka je makaranta, kuma Jihar Bauchi ita ce ta huɗu a yawan makarantun firamare da ke amfana da shirin, wato ta bi bayan jihohin Kano, Binuwai da Kaduna. Haka kuma Kano ta fi kowace jiha yawan yaran da ake ciyarwa, daga ita sai Katsina, Kaduna, Neja, Jigawa, Binuwai, kafin Bauchi.”

Anibeze ta ce ministar, wadda Babban Sakatare ya wakilta, kwanan nan ta ƙaddamar da shirin Agajin Agajin Kuɗi ga Marasa Galihu a ranar 4 ga Yuli, 2022 a garin Oshogbo na Jihar Osun.

Ta ƙara da cewa: “Ya kamata wannan ƙungiyar ƙaryar ta faɗa wa mabiyan ta abin da ya sa Hajiya Sadiya Farouq ba ta fara rabon kuɗin ga mabuƙatan da ke Jihar Bauchi ba.

Ta ce: “Sadiya Umar Farouq ‘yar siyasar Nijeriya ce wadda ba ta damu da ƙabilanci ba, sannan uwa ce kuma matar aure, mai taimakon jama’a kuma Musulmar gaske. Ta na raba kayan agaji daidai wa daida ga talakawa mabuƙata ba tare da la’akari da jihar da mutum ya fito ba ko yaren sa ko addinin sa.

“In ba domin kada a ce mun ƙyale ba, to, da wannan ma’aikata ba ta ɓata lokacin ta da kuzarin ta har ta kula kashi ba wajen maida martani ga wannan ƙazamin rahoton na wannan sakaryar ƙungiyar ta ‘yan neman ganin bayan mutum, to amma mun ga ya dace a gyara ɓarnar da su ke son aikatawa.

“Sadiya Umar Farouq dai ‘yar asalin Jihar Zamfara ce wadda ke auren tsohon Hafsan Hafsoshin Mayaƙan Sama, Eya Mashal Abubakar Sadique. Kasancewar ta matar ɗan Jihar Bauchi ya ba ta damar da duk wata mace ‘yar Bauchi ta ke da ita.

“Saboda haka, wannan ƙungiya mai suna ‘APC Initiative for Good Governance’ wadda ba a san ta ba kuma ba ta da rajista, ba za ta iya hana ta shuka ko cin moriyar wani alheri na cigaban jihar mijin ta ba daidai da haƙƙin jihar a kason da ma’aikatar da ta ke jagoranta ta bayar, kuma duk wata kutungwila da ƙarya da aka shirya ba za su hana ta mara wa mijin ta baya ba a ƙudirin sa na siyasa.

“Babu wani lokaci da Sadiya Umar Farouq ta taɓa karkatar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwa na jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya zuwa Bauchi, kuma ba ta taɓa barin ayyukan ofis da su ka rataya a wuyan ta ba ta koma Bauchi.

“Akasin hakan ma, ta na aiki ba tare da gajiyawa ba kuma bilhaƙƙi da gaskiya wajen tabbatar da cewa babu wani mabuƙaci ɗan Nijeriya da aka bar shi cikin yunwa, tare da nufin ɗaga matsayin su daga inda ta same su.

“Mai girma Minista, jim kaɗan bayan ta ƙaddamar da Shirin Bada Tallafin Kuɗi Ga Mabuƙata, ta tafi Saudiyya domin sauke farali, tare da amincewar mai girma Shugaban Ƙasa, kuma ana sa ran dawowar ta bakin aiki a wannan makon.

“Ba mu damu da yanayin da ƙungiyar ‘APC Initiative for Good Governance’ ta samu kan ta a ciki ba na firgicin ganin martaba da manyan nasarorin da ministar ke samu, domin dai ita babban abin da ke gaban ta shi ne ta sauke nauyin da aka ɗora wa ma’aikatar ta.

“A yayin da Sadiya Umar Farouq ta fuskanci alƙibla tare da jajircewa kan muradin mai girma Shugaban Ƙasa na ƙarfafa rayuwar ‘yan Nijeriya ta hanyar fito da shirye-shirye daban-daban don tabbatar da an kula da kowane mabuƙaci ɗan Nijeriya, sai ga wasu marasa aikin yi waɗanda siyasa ba ta yi da su a Jihar Bauchi, waɗanda ba su da wata gudunmawar alheri da za su iya kawowa, sun koma zaman haifar da rikici maras alfanu, su na haifar da saɓani da rashin jituwa, su na ɓata lokacin su wajen sarar mai girma Minista.

“Su kuwa talakawa mabuƙata, waɗanda saboda su ne aka kafa Ma’aikatar Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, su na murna da kyakkyawan shugabancin da Sadiya Umar Farouq ta ke yi. Ta na aiki tuƙuru domin a rage fatara a ƙasar nan, kamar yadda mai girma Shugaban Ƙasa ya ƙudirci ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara.

“Ministar, da ma’aikatar ta, ba su damu da irin waɗannan ƙananan maganganun da ake kitsawa ba, kuma ko kaɗan ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙoƙarin da su ke yi na tabbatar da sun kawo waraka ga mabuƙatan ƙasar nan.”

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *