A yanda mutane suke tunanin ya kamata mawakiya SAFA ta daina yin irin abubuwan da takeyi a yanzu akan suna ganin bai dace ba.
Ita kuma da bakinta tace: “Ina so na zama kamar Davido” lokacin da tayi hira da shafin BBCHausa.
Kamar yadda shafin BBCHausa ya rawaito Safara’u ta ce babban burinta a rayuwa shi ne ta ga ta zama kamar shahararrun mawakan kudancin Najeriya kamar Davido da Burna Boy da kuma ganin ta sami kyautar mawaka ta duniya Grammy saboda ‘‘Mu nan arewa ban taba ganin wanda Kudu suka kira shi yaje yayi wasa, amma za ka ga an kira su Tiwa Savage da P-square da Rikado da sauransu’’.
Sannan Jarumar ta ce ita dama ba barin harkar fim ta yi ba illa kawai hutu da ta dauka domin mayar da hankali kan waka.
Ta ce a yanzu haka ma suna shirin fara wani fim mai dogon zango ita da abokin wakarta Mr 442, kuma su za su shirya fim din da kansu.
Akan maganar kalubale da take fuskanta
Safara’u ta ce ba ta fuskantar wani kalubale daga wajen iyayenta saboda waka da ta fara a yanzu da kuma fim da take yi a baya dukkansu sai da ta nemi yardarsu kafin ta fara, inda kuma ‘suka ce na je nayi tun da sana’a ce kuma na kiyaye a kan duk abin da nake yi,’’. Ta ce tafi son wakar ‘Inda ass’ a cikin wakokinta, BBCHausa ta rawaito.
Akan maganar hukumar Hisbah tana nemanta
Ta kuma kara da cewa maganar da ake yi cewa hukumar Hisbah ta gayyaceta ita dai bata san da wannan zance ba saboda kafofin sada zumunta ne kawai suka yi ta yayata batun.
In baku manta ba dasu mun kawo muku cikakaken bidiyon hirar da shafin BBCHausa sukayi da ita mawakiya SAFA, zaku iya kallon bidiyon ta hanyar danna nan.
Kamar yadda kuka sani a watannin baya ne bidiyon tsiraicin Safara’u, mai fitowa a shirin Kwana Casa’in da Arewa24 ke shiryawa, ya fita duniya.
Wanda bayan fitar bidiyon, masu shirya fim din sun dakatar da ita daga shirin lamarin da ya sa ta tsunduma cikin harkokin wakoki.