• Mon. Jun 17th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Banyi Rigima Da Dan Garuwa Ba, Hakkina Na Karba A Wajensa Na Barnar Da Yayi Mun – Aminu Sharif Momo

ByLucky Murakami

Aug 25, 2022

Bayan wani bidiyo da yayi ta yawo a shafkuna sada zumunta wanda mutane da yawa suna zagin momo akan abinda ya aikata domin babu wanda ya taba tinanin cewa momo zai aikata wannan abu kamar yadda tunanin mutanen ya nuna musu wanda suke daukar bidiyon da wanda suke a wajen.

Tunanin mutane dai a yanzu haka ya karkata kan jaruman kannywood wanda sun kasance suna abinda suke ganin ya dace hakane yasa momo ya karbi kudi a wajan Wani bawan allah daya bugar Masa mota a yanzu haka ga Video ka kalla.

Bayan faruwa wannan lamari shi jarumi momo yayi magana inda yace shi baiyi rigima da dan garuwa ba, ya dai san kawai yace masa sai ya biyashi barnar da yayi masa kuma bai hakura ba sanda ya biyashi.

Ya dai fito ya baiyana gaskiya kan zargin da mutane suke masa na cewa yace har cikin kasuwar singa yayi rigima da dan garuwa.

Ya  kara da cewa dan garuwar yayi masa barna ne a motarsa kuma yaga bazai iya hakura ba saboda gangancin wannan mutumin, inda ya naimi ya biyashi kudin barnar.

Kamar dai yadda ya baiyana a cikin bidiyon dan garuwan ya biya momo naira dubu goma na wannan barna da yayi a matsayin kudin gyaran motar momo.

Mutane da dama dai sunyi ta sukar momo inda wasu suke cewa wannan abinda yayi rashin tausayi ne da rashin imani, a yayinda a wani gefe kuma wasu mutane suke cewa yayi daidai.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *