Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Batun Lalata Dan Yan Matan Jami’a Gaskiya Tayi Halinta

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiOctober 30, 2022No Comments2 Mins Read

    Abunda zan rubuta yanzu da yawa cikin Malaman jami’ah sun san haka yake, amma galibi kowa zai kauda kai ne saboda gudun zargi, ko kuma kar ace yana baiwa cutar da dalibai kariya. Duk da yiwuwar hakan, ba zai hanani bayyana abunda na sani ba, saboda shi ma wani ilimi ne da boye shi ya kan iya zama nau’in zalumci.

    Ina son mutane su gane cewa a ka’idar jami’ah; ba laifi ba ne Malami yayi soyayya da dalibar shi mace. Malamai da dama sun yi soyayya da daliban su mata har sun yi aure har da y’ay’a. Ko a jami’ar da nake aiki an yi irin wannan aure da dama kuma Allah ya albarkace su da zurri’ah.

    Ita Jami’ah babban wajibine gareta ta kare hakkin dalibai da Malamai daga cin zarafi kowanne iri ne, saboda haka tilas ne hukumar Jamiah ta tabbatar da cewa ba tilas ko barazana aka yi wa daliba ko dalibi ba. Idan ko babu tilas cikin abunda ya faru; shikenan magana ta zama zabin mutane biyu masu hankali.

    Bisa shekarun da na yi ina aiki a jami’ah na san cewa ba lallai ne irin wannan halayya ta nema tsakanin Malami da daliba ya zama laifin Malamai kadai ba. Su ma dalibai mata suna taka rawa mai yawa wajen gabatar da kawunan su wajen Malaman na su. Hakanan kuma yadda dalibar kan iya yarda da Malamin shi ma Malamin kan iya yarda da dalibar.

    Sannan wannan video ya nuna cewa dalibar ta kai kan ta ne da niyyar Jan hankalin Malamin, sannan ta yi sintiri wajen shi har sau uku, duk abunda ya fada tana amincewa da shi, ina gani ko Sarkin gari ne za’a iya kamawa a wannan yanayi ba Malami kadai ba. To ta yaya wannan video zai zama cikakkiyar hujja akan Malamin? Sai dai a kama shi da laifin “abusing office” amma sexual harassment kam ina ganI yarinyar ce ta bashi kofa, Lamar yadda dama mun San cewa manufar ta kenan.

    Saboda haka ina bada shawarar cewa yadda aka samu yan jarida suka yi kyakkyawan bincike akan yadda wasu Malaman jamiah ke amfani da damar su wajen bata yara mata, akwai bukatar irin wannan bincike wajen gano shin dalibai matan ma kan iya haddasa irin wannan halayya?

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.