• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Bayan Bankin Duniya Ya Dauki Nauyin Karatunta Yan Jarida Sunyi Hira Ta Yarinya Mai Baiwar Lissafi

ByLucky Murakami

Aug 7, 2022

Wani labari daya shigo mana ya tabbatar mana da cewa Saratu Dan-Azumi, wata ‘yar matashiya daga jiharKano ta sake samun daman gurbin karatu saboda kwakwalwan da Allah ya bata na kwarewa a fannin Lissafi.

Kwanan nan aka gano cewa yarinyar ashe ba ta zuwa makaranta amma duk da haka tana iya lissafin lambobi kamar mai aiki da kwanfuta,wanda har ta yi nssarar samun talafin karatu daga gidauniyar Bashir Ahmad, BAF.

Mutane da dama sun yi ta tsokaci tare da bayyana jin dadinsu game da irin baiwar da Allah Ya yi wa Saratu, ’yar asalin kauyen Gwadayi, Gundumar Shagogo a Karamar Hukumar Gaya ta Jihar Kano.

Bidiyon Hira Da Yarinya Mai Baiwar Lissafi Da Ta Samu Tallafin Karatu Har Zuwa Jami’a

https://www.youtube.com/watch?v=clyuCUsKdz8

Tallafin Da Saratu Ta Samu

Saratu ta samu tallafin ne a karkashin shirin tallafawa mata don su yi ilimi (AGILE), wanda Bankin ke daukar nauyi a jihar Kano.

Amihad.com ta samo wannan labari ta hanun Malam Aliyu Musa, Jami’i Yada Labarai na shirin wanda shine ya bayyana haka ga Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba.

Malam Yusuf wanda kuma shi ne Mataimakin Daraktan yada labarai na Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ya ce, ofishin kula da shirin na Bankin Duniya a jihar Kano ya bayar da umarni a zakulo yarinyar nan a kuma sa ta a makaranta.

“Sai a ka yi sa a, masu kula da shirin ilimin mata na AGILE na tsaka da ziyara zuwa masarautu biyar na jihar Kano don neman hadin kan sarakuna kan batun ilimin mata a jihar,” inji shi.

A yayin ziyararsu a masarautar Gaya ne jami’an suka yi wa Sarki bayanin yarinyar da kuma aniyarsu ta daukar nauyin karatunta, sai Sarkin na Gaya ya sa aka zo da yarinyar da kuma iyayenta har gabansu.

Nan take wakilin a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano, Malam Haruna Mohammed Pandau, ya ba Saratu kayan makaranta da jakar makaranta da kuma wasu kayayyakin karatu.

Shi kuma Ado Tafida Zango, mai kula da shirin AGILE a jihar, ya ba ta Naira 20,000 daga aljihunsa don taimaka wa karatun nata.

Muna fatan Allah ya kara bawa yaranmu nasara.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *