Kamar yadda kuka sani Fati Muhammad tsohuwar jarumar kannywood wacce ta dade tana zamani a shekarun baya kafin tayi aure.
Auren jaruma Fati Muhammad yasa aka daina ganin ta a fina finan da ta saba fitowa, sai dai kuma daga baya auren ya mutu wanda shine fitowarta na biyu da ga gidan auren mazaje daban daban.
A hira da akayi da ita a wani shiri mai suna daga bakin mai ita, Fati Muhammad ta bayyan wasu shirrruka da suka shafi rayuwarta.
Daga bakin mai ita wani shiri ne na BBCHausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.
Kamar yadda binciken mu ya tabbar a wannan kashi na 35, shirin ya tattauna da shaharrariyar tauraruwar fina-finan Kannywood Fati Muhammad wadda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta.
A cikin tattaunawar, ta yi waiwaye kan dalilan da suka sanya ta soma harkar fim, da irin rawar da ta fi takawa, da ma wanda ta fi so a hada ta da shi a fim.
Kazalika ta yi magana kan abin da ba za ta taba mantawa da shi ba, da kuma shigarta harkokin siyasa, har ma da nau’in abincin da ta fi so ta ci.
Ga cikakken bidiyon nan a kasa sai ku kalla don saurarar hirar baki daya.
Bugu da kari, kamar yadda wasu mutane suke ta magana kan cewa dama duk tashen wata jaruma kafin tayi aure ne. Da zarar tayi aure to mutuncinta shine ta zauna a gidan mijinta.
Duk wacce ta kashe aurenta ta fito, to ko ta dawo harkar fim taurarawar ta bazata sake haskawa kamar yadda tayi a baya ba.
Hakan kuma ya faru da wannan jaruma duk da cewa bata ce ta dawo harkar fim gadan gadan ba. Amma dai abubawa da yawa da suka shafeta sun tabbatar da hakan.