• Sun. Dec 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Bazan Daukaka Kara Ba, Na Amince Da Hukuncin Kotu Akan Mazabar Yobe Ta Arewa – Lawan

ByLucky Murakami

Sep 29, 2022

Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Lawan ya ce ba zai daukaka kara ba kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Damaturu a jihar Yobe ta yanke ranar Laraba kan zaben Sanatan Yobe ta Arewa da ke gabatowa ba.

Sanata Lawan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwar manema labaru wadda ya sanya wa hannu kuma ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce ya amince da hukuncin da kotu ta yanke na hana shi takara da kuma shiga zaben.

A cikin sanarwar ya kara da cewa, “A jiya Laraba 28 ga watan Satumba, 2022, babbar kotun tarayya dake Damaturu ta yanke hukunci kan wanda ya cancanta ya tsaya takarar Sanatan Yobe ta Arewa a zaben 2023. Wanda hukuncin da aka ce ya hana ni tsayawa takara don haka na shiga zaben.”

“Wanda bayan tuntubar juna da abokanan siyasa da magoya bayana da sauran wadanda suka dace na tuntuba, na yanke shawarar ba zan daukaka kara kan hukuncin ba, na amince da hukuncin.”

“A halin da ake ciki, ina ganin ya dace in gode wa mai girma Sanata Ibrahim Gaidam bisa rawar da ya taka a siyasar jam’iyyar APC a jihar Yobe, ina kuma gode wa mai girma Gwamna Mai Mala Buni bisa goyon bayan da ya bani tare da nuna yanuwantaka.”

“Ga kuma al’ummar mazabana, ina gode muku baki daya bisa goyon bayan da kuka bayar, da biyayya da sadaukarwar da kuka yi na gina al’ummarmu da yankin Yobe ta Arewa da ma jihar Yobe baki daya.”

“Ina so in kara tabbatar muku cewa zan ci gaba da yi muku hidima a cikin kaina da kuma kowane irin aiki a kowane lokaci.”

“Mun yi tafiya tare tsawon lokaci, kuma wannan tafiya za ta ci gaba da zama doguwar tafiya mai tsawo, dangantaka ce mai ban sha’awa kuma ba za ta iya yin karfi ba. Ina bin ku duka, Alhamdulillah.” In ji Sanata Lawan.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *