Wata mata yar kasar Congo ta auri maza biyu hakan ya girgiza mutane, duba da cewa mata ba su cika yawan auren maza biyu a Afirka ba.
A gida daya dukkansu ke zaune Polyandry shine tsarin da mace ke auren maza biyu kuma dukkansu su rika zama a gida daya.
Ta fada wa Afrimax English a wani hira cewa:
“Saboda wahalhalun rayuwa, mutumin ya yi tafi kuma bai dawo ba. Na tsinci kai na cikin kadaici, na shafe shekaru uku da rabi ni kadai ba tare da miji ba.”
Mijin ta na farko ya dawo Ta bayyana cewa: “Bayan wannan shekarun na rasa shi kuma na fara soyayya da wani mutum. Bayan shekara daya, mijin na farko ya dawo.”
Jisele ta ce ba ta yi tsamanin mijinta na farko zai dawo ba bayan shekarun nan masu yawa.
Albert Jarlace ya ce: “Na hadu da wannan matar lokacin da na ke aiki a ma’aikatar hakar ma’adinai kuma ta fada min tana da wani miji da yadda ya bar ta ya tafi duniya don neman rayuwa.”
Ya kara da cewa: “Na ga kaman ba ni da zabi saboda muna tare kuma na zauna da ita ba tare da sanin tana da wani miji ba.”
Da Murula ya dawo ya yi fada da Jarlace yana cewa Jisele matarsa ce Jarlace ya ce: “Matar ta ce kada in rabu da ita. Don haka na ga ya dace in tsaya da ita yanzu kuma mun haifi yaro daya.”
Murula ya kara da cewa: “Tuko watatu (maza biyu ne ke nan). Ba mu da matsala, wannan matar mu ne. Tunda na bar gida ban yi magana da matata ba ko sau daya. Da na dawo, na tarar da ita tare da wani mutum.”