• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Bidiyon Mai Wushirya Yana Rungumar Murja Ya Jawo Musu Matsala Wajen Mutane

ByLucky Murakami

Oct 9, 2022

Wannan abubuwan da wa’yannan yan tiktok din suke abin nasu ya fara wuce gona da iri tun ana ganin Kamar bawai wani abu suke ba illa kawai abinda sukasan zasu bawa mutane ɗariya da kuma wanda zai kara jawo musu yawan masoya wato mabiya a shafinsu shi suke ashe ba haka bane.

A kwana biyu da suka wuce nan ma an gansu a wani video wanda yake ɗalibta suna ta wani abu wanda sam wannan abin bai dace da dabi’ar addini ba da kuma al’adar malam bahaushe ba tunda suma ansan cewa Dukansu hausawa ne amma kuskure abinda suke aikatawa tare bayan kuma babu ɗaya daga cikinsu wanda yake muharramin daya kawai haifuwar social media ce.

Tunda murja taje abuja ta dawo bata da wani aboki wanda ya wuce wannan mai wushirya wanda har kofar gidansu yake zuwa domin ya jirata su tafi harkokinsu na daukar video wanda za’a ana sawa a Tiktok.

Basu taba wani video wanda yaja musu magana ba kamar wannan ba domin anga yadda kake rike da hannun ta bayan hakan sunsan ba karamin abin kunya bane domin koda yan Film ne sukayi haka an dinga yamadidi dasu kenan balle kuma yan tiktok wanda ake ganin yanzu sunfi kowa nuna fitsara a kafofin sadarwa na zamani wanda wasu suke fatan a kulle wanan abu saboda yadda yake bata tarbiyyar yara.

Ana ganin dai yanzu shikkenan Maganar aure babu ita tunda a baya anji yadda angon Ummi Rahab wato Lilin Baba yayi musu alkawarin daular nauyin auren su matukar sun amince zasu aure juna.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *