• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Bidiyon Martanin Naziru Sarkin Waka Ya Fusata Yan Pi Network

ByLucky Murakami

Sep 13, 2022

Sarkin wakar tsohon sarkin Kano wato naziru Sarkin waka yayi wata magana wacce ake ganin kamar zata iya jawo masa bakin jini a wajen samari harma da yan matan domin yanzu kusan duk saurayin daka taba sai kaji yace Pi network yake jira ta fashe ya samu wasu kudade yabar wannan kasar ya koma kasar waje da zama gaba daya.

 

Sai dai yau dinnan Sarkin waka yayi wata magana wacce azahirin gaskiya masu wannan abun basu dadi ba saboda yadda suke girmama shi da kuma ganin mutuncinsa amma yazo ya faiyace gaskiya akansu wanda basu ji dadin hakan ba.

Sarkin waka yace duk wani saurayi da yake jiran Pi ya fashe ya yaudari kansa wanda daga karshe ma ya kirasu da mahaukata wanda wannan kalmar ba karamin ciwo tayiwa matasa ba da duk wani wanda yake jiran wannan harkar yaji haushi wannan maganar.

Jin kadan bayan fadan wannan maganar har an samu wasu matasa wanda suka fara mayarwa da Sarkin waka martani inda suke cewa sudai basa maula kuma basa roko a waka wanda duk wanda yaji yasan cewa da wannan mawakin suke domin shi kadai ne yake wa’yannan abubuwa.

Ga cikakken bidiyon sa nan sai ku kalla:

Amma kuma kome zasu mayar masa bazasu rama abinda ya fada musu domin duk wanda ya kira ka da mahaukaci ya riga ya gama dakai saboda babu wata kalma wacce takai ta mahaukaci ciwo a wajen mai hankali.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *