Bayyanar bidiyon fitacciyar jaruma Rahama Sadau lokacin da take wajen mosta jiki ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta.
Mutane suna ta tofa albarkacin bakinsu bayan da sukaga an wallafa bidiyon jaruma Rahama Sadau tana motsa jiki sanye da kayan atisaye.
Wasu mutane suna nuna rashin jin dadinsu ganin kalar kayan da ta sanya lokacin da take mosta jiki inda suke alaqanta hakan da bai dace ga mace musulma ba ta shiga cikin maza sanye da wadannan kaya domin motsa miji tare.
Da yawa sun alaqanta hakan da sam sam bai dace ba, inda daga wani bangaren kuma wasu mutane suna cewa basu ga wani abun aibu ba na wannan abu da tayi kawai hali ne na mutanen mu komai suka gani bazasuyi shiru ba sai sunce wani abu.
Bugu da kari, cikin wannan bidiyo babu wata shiga ta rashin da’a da tayi na kayan da ta sanya domin kuwa har hula ta sanya da kuma dogon wando.
Amma dai duk da hakan baisa ta tsira daga martanin mutane ba saboda basu saba ganin irin wannan ba.
Ga bidiyon nan ku kalla mun kawo muku shi a kasa.
Idan kun lura da kyau sai kuzo ku ajiye ra’ayinku akan wannan bidiyo.
Shekaru 14 anan nake debowa mahaifiyata ruwa saboda itace rijiya a Qauyenmu Inji Rahama Sadau
Rayuwarta Ta Baya Takecewa A shekaru Goma sha Hudu Da suka Gabata Ta nuna wani tsohuwan rijiya datake devowa mahaifiyarta ruwa.
Kamaryanda Shafin Nishadi Ya ruwaito Kamar hakan aruma Rahama Sadau ta wallafa wadansu hotuna, inda ta nunawa masoyanta da mabiyan ta wata rijiya a kofar gidan mahaifiyarta, wacce a cewar ta; a cikin rijiyar ta ke diban ruwa, shekaru goma sha 4 da suka gabata.
Rahama sadau ta duki hotuna a kauyen da rijiyar take wato inda mahaifiyarta take zaune da a cikin yanayi na nishadi, jaruma Rahamar ta dauki hotunan a kauyen dake jihar Gombe wanda tace anan ne ta taso, kuma anan tayi kuruciya ita ta mahaifiyar tata.
Babban abin da ya baiwa wasu daga cikin mabiyan ta mamaki, shine yadda jaruma Rahamar ta dauki hotunan a garin kuma har ta yada su, tana mai ikirarin cewa ta dibi ruwa a wannan rijiyar shekara goma sha 4 baya.
Jarumai irinta suna jin kunyar bayyana bayan su saboda ba kasafai aka fiya ganin manyan taurari suna nuna wani abu da suka yi a baya ba, musamman idan na wahala ne amma ita tayi hoto ta wallafa, saboda yanzu sun sami daukaka, kuma idan suka bayyana bayan su, kamar za’a yi musu dariya ne, ko kuma suna ganin yanzu sun girmi wancan yanayin na baya.
Dalilin haka wadansu sukan nuna dama su daga babban matsayi suka taso, koda kuwa sun sha wahala a baya. Amma ita Rahamar hakan ko a jikin ta.
Daga gida ake fara samun tarbiyya, Inji Rahama Sadau, sau da yawa akan ce wasu jaruman Kannywood suna yin wasu abubuwan da gayya don a dinga cece-kuce akansu wanda wasu ke ganin hakan ne kasuwancinsu.
Wasu na ganin idan har ba a maganar jaruman, kasuwarsu ta mutu. Hakan ke sa wani lokacin da kura ta lafa sai su kara taya da sabuwa bayan wani dan lokaci, Nishadiii blog taruwaito kukasance damu.