Wani yaro ya hau kan gadar kofar Nasarawa dake jihar Kano ya samu waje ya makale yace bazai sakko ba sai Buhari ya sauka a mulki.
A jiya Jama’a ne kano suka wayi gari da faruwar wani bakon al’amari na Wani Dan Karamin Yaro Daya hau Saman gada yace bazai sauko ba harsai Buhari ya sauka daga mulki.
Hakan yasa mutane da dama sukazo suna kallon ikon Allah wasu na daukar hotuna, wasu na daukar bidiyo, wasu kuwa mamaki ma hanasu yin koamai.
Shi dai wannan Dan Karamin Yaro kamar yadda zaku gani a cikin bidiyon dake kasa ya shige Chan Cikin wani lungu ne a gadar inda ya makale a wajen kuma yaki saukowa.
Saidai daga baya yaron yafito daga cikin lugun saidai yaki ya sauko, wanda a nan ne mutane suketa daukarsa da wayoyi domin mamaki. Gadai bidiyon nan ku kalla da idonku kada a baku labari.
Sanin kowane dai irin halin ha’ulain da mutanen cikasarnan suke ciki, na rashin zaman lafiya da kuma tsadar rayuwa.
Allah yakawo mana sauki, kuma ya zaba mana shugaba mafi Alkhairi a shekarar 2023.