Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa fursunoni 90 afuwa ciki har da mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa.
Gwamnan ya aiwatar da hakan ne sakamakon bikin Babbar Sallah.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gidan gyaran hali na Najeriya reshen Jihar Kano Musbahu Lawan K Nassarawa ya saka wa hannu, gwamnan ya biya wa mutum 77 diyyar kuɗin da ake binsu domin fita daga gidan gyaran halin haka kuma akwai mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa a baya da halayansu aka gamsu da su wanda hakan ya sa gwamnan ya yi musu afuwa.
Haka kuma akwai fursunoni uku da aka yanke wa hukuncin kisa da gwamnan ya yi musu afuwa aka mayar da hukuncinsu ɗaurin rai da rai.
Gwamna Ganduje ya kuma bai wa fursunonin shanu da raguna da shinkafa domin su ji daɗin Babbar Sallah.