Budurwar nan wadda tayi magana akan Mallam Daurawa ta sake kiran ruwa inda tace “duk namijin daya auri macen da tafi karfinsu jaki ne” wanda maganar ta fusata mutane matuka.
Lallai wannan mata da magana mai muni take ita a kullum maganar da take fada gani take Kamar kare martabar mata take wanda kuma natasani ba hakan kamar kara furkusar da girmansa take ba saboda duk wata mace duk girmanta da kudinta tofa matukar suna tare da mijinta tofa wannan mata ta zama kamar sitiyarin mota sai yadda yayi da ita kuma Allah nema ya nuna haka saboda haka babu Wanda ya isa ya canja hakan.
Amma a duk lokacin da wannan matashiyar zatayi magana sai tana nuna cewa ita ai wayayyiya ce ko kuma ba Sa’ar kowanne namiji bace saboda yadda take ganin kamar tana da matukar kyau saboda haka sai wanda ta tabbatar da cewa yafita sannan zata aure wanda kuma hakan ba daidai bane kuma bazata taba cika birintata ba matukar tanada wannan tunanin akanta.
Ga bidiyon nan dai sai ku kalla don saurarar abinda wannan budurwa ta fada.
Idan baku mantaba itace a kwanakin baya wani babban Malamin addinin Muslunci a jihar Kano ya fadi wata magana wacce bashine ya kirkire taba shima karantawa yayi a wasu littattafan addini amma wannan budurwa tazo tana kalubalentarsa a wanda a wannan lokacin tasha zagi da bakaken maganganu a wajen mutane.
Tace duk wani namiji wanda ya auri mace wacce tafi karfinsu jaki ne wanda wannan maganar tata tayi tsauri kuma tayi zafi inda wasu ke cewa akwai fitsari da kuma rashin kunya aciki tunda an tabbatar da cewa mace bata taɓa fin karfin namiji a haka tsarin halittar yake Allah ne ya banbanta tun a halitta.
Amma wasu sun fassara wannan maganar ta wata ma’ana daban wanda suke ganin cewa manufarta shine indai kasan zaka auri yarinya amma kuma ka kasa ciyar da ita irin abubuwan da iyayenta suke ciyar da itaba to hakika wannan macen tafi ƙarfin ka kuma ka cuceta.