• Thu. May 23rd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Budurwar Da Take Saida Kwalam Da Kayan Makulashe Don Rufawa Kanta Asiri

ByLucky Murakami

Aug 13, 2022

Wata matashiya a jihar Sakkwato da ke Najeriya, ta cire girman kai inda ta rungumi sana’ar yin kayan kwalam da makulashe domin rufa wa kanta asiri.

Rukayya Abubakar Bajah matashiya ce da ke ajin karshe a jami’a, amma kuma ta rungumi sana’ar kayan makulashe, inda take yin gullisuwa da kwakumeti da carbin malam da makamantansu.

Matashiyar dai ta rungumi sana’ar ne a wani mataki na kaucewa rashin aikin yi da kuma dogaro da kai.

A cewar matashiya Rukayya Bajah ta samu alkhairi mai yawa sakamakon sana’ar tata, kuma tana daukewa kanta kudin makaranta da sauran lalurorin yau da kullum, baya ga matasa da take koyawa sana’ar da kuma wadanda ke taimaka mata suke kuma cin abinci a karkashinta.

Ya Kashe Kaninsa Bayan Ya Kamashi Yana Zina Da Matarsa

Wa ya kashe kaninsa, yayin da ya kamashi yana Zina da matarsa(Turmi da Tabarya) a Abuja.

Lamarin ya farune a unguwar Kubwa dake babban birnin tarayya, Abuja.

A daren ranar Larabane, Abdullahi Yusuf ya kama kanin nasa yana masa cin amana da matarsa.

Aikuwa bai yi wata-wata ba, ya dauko wuka ya caka masa.

An dai kama Abdullahi Yusuf, ya kuma shaidawa manema labarai cewa, matar tasa tace zata je makwabta wamda daga canne sai kanin nasa ya bita gidan makwabtan.

Da ya ji shiru shine ya bi sahu, ai kuwa yana zuwa ya shiga dakin da matar tasa take, sai ya gansu tsirara suna lalata.

Wani shaida, Olugbenga John, yace bayan da Abdullahi Yusuf ya kashe dan uwansa, ya so tserewa amma suka kamashi suka kira ‘yansanda.

 

Anyi Auren yar autar marigayya Jaruma Amina Garba Dumba

Allahu akbar tsohuwar jaruma a masana’antar kannywood wacce ta rasu dadadewa wato Hajiya Amina Garba Dumba anyi auran yar ta wacce itace yar auta acikin ya’yan da jarumar ta haifa a duniya kuma tayi aura sun tare tare da mijinta.

Yarinyar da bata wuce shekara ashirin ba itace yar kara wacce jarumar ta mutu ta bari a duniya wanda lokacin da ta rasu tana karama nata iya mallakar hankalinsuba sai gashi cikin ikon Allah yanzu ta zama amarya acikin sabuwar Shekarar nan.

An daiga manyan jarumai mata da maza a wajen taron bikin musamman ma matan na kannywood wanda sune sukayi uwa kuma sukayi makarbiya acikin sha’anin bikin kuma angansu suna chashewa wanda hakan ba karamin sha’awa ya bawa mutane ba.

Ganin karar da jaruman kannywood din sukayiwa marigayyar yasa mutane suke ta yabonsu domin koda tana raye itakacin abinda zasuyi kenan sai gashi dukda bata Nan sunyi abin a yaba musu.

Sai dai kuma kash mutane daba’a iya musu saida suka soki jaruman inda sukace ai su jaruman inda sabga ce ta biki tofa anan sukafi karfi inda za’a ga suna rawar jiki dakai mari wajen anyi komai dasu saboda shagalarsu.

Amma kuma abinda mutane basu duba ba shine yariyar fa da akayiwa bikin yar tsohuwar jarumar wasan kwaikwayo ce aiki bakomai sayi kara wajen halattar bikin Allah ya jikan mahaifiyar ta da rahama ya kuma bata zaman lafiya agidanta.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *