• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Da Dumi Duminsa Shugaba Buhari Ya Gano Gidan Jarida Biyu Da Suke Bashi Ciwon Kai

ByLucky Murakami

Jul 28, 2022

Da Dumi Duminsa: Gwamnatin Najeriya Za Ta Dauki Mataki Akan BBC da Jaridar Aminiya

Shugaba Buhari ya ce sam ya gano daya daga cikin hanyoyin da ke ta’azzara matsalar tsaro, ya ce zai yi maganin BBC da Aminiya.

Bayan kai ruwa rana da Twitter, gwamnatin Buhari za ta sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama tsageru.

[ads1]

Lai Mohammad, ministan yada labarai da al’adu ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis.

Me za ku ce?

Buhari Bai San Da Labarin ‘Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Shi Ba Saida Na Fada Masa, Cewar Gwamna El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce shi ne ya sanar da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari game da barazanar da masu ikirarin jihadi suka yi cewa za su kama Shugaban da shi Gwamnan.

Gwamma El Rufa’i ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ‘yan jarida da ake yada wa kai tsaye, jiya Laraba da daddare.

[ads1]

Idan dai ba a manta ba a karshen makon da ya gabata ne masu ikirarin suka fitar da wani biidiyo da ke nuna mutanen da suka sace na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, tun a watan Maris inda a ciki suke barazanar cewa sai sun kamo shugaba Buhari da gwamna El-Rufai .

El Rufa’i ya ce shi Buhari bai ma san da wannan barazana ba sai da ya gaya masa, sannan kuma Gwamman Jihar Zamfara Bello Matawalle ya ka wa shugaban hoton bidiyon ya gani.

Gwamna Elrufai ya ce daman shi tun a baya an gargade shi da ya yi hankali shi da iyalinsa a kan wannan barazana.

Ya ce, ‘’Ta yaya za mu kasance a kasar da take da sojoji da ‘yan-sanda da gwamnatin tarayya amma kuma wasu ‘yan ta’adda su rika barazanar za su sace shugaban kasa?’’

Gwamnan ya ce ai shi daman tun baya da shekara biyar yake bayar da shawara da a shiga dajin a yi wa sansanoninsu ruwan bama-bamai, da cewa ta hakan ne za a yi maganinsu.

Ya ce ya gana da Shugaba Buhari ne a ranar Lahadi inda ya gaya masa yadda girman wannan matsala ta tsaro yake.

[ads1]

Ya yi bayani da cewa, idan a baya wadanda ke cikin gwamnati suna daukar wannan abu da wasa, suna ganin abin na faruwa ne kawai a Katsina da Zamfara da Kaduna da Naija, to yanzu abin ya zo har gida, saboda haka dole ne a tashi a ga bayan mutanen nan.

Yanzu dan Allah jama’a a haka zamu rayu a irin wannan yanayin da wasu ke hallaka al’umma sannan suna barazanar kama shugaban kasa da gwamna.

Muna rokon Allah ya azurta kasar mu Nijeriya da zaman lafiya mai daurewa.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *