News

Daga Karshe An Fara Karatu Gadan-gadan A Makarantun Mata da Maza Da Aka Raba A Bauchi

Mun gode wa Allah da ya karbi addu’o’inmu na fara tsarin makarantun sakandare na mata-zalla kamar yanda aka tsara a Jaharmu ta Bauchi.

Ranar litinin da ta wuce, ilahirin makarantun da aka fara da su a garuruwa dabam dabam a jahar sun bude kuma y’an makaranta sun je makarantunsu. Ga hotuna na makarantun a yanda suke jiya Talata. Alhamdulillah.

Za mu yi amfani da wannan satin a matsayin gwaji da karban koke koke daga iyaye da dalibai a bisa makarantun da aka tura su ko rashin fitar sunayensu a jadawalin tura daliban. Daidai sai Allah.

Yamadidi

Mun lura da yamadidi da karin gishiri wanda wadanda ba sa son shirin suka rika yi don wasu yara kamar 50 daga makarantu biyu a garin Bauchi (GDSS na Kofar Idi da Kofar Wambai) sun yi zanga zanga ran Litinin kan tura su GCDSS Bauchi.

Da ma duk tsari mai kyau ba ya rasa kalubale ko me kashinsa. Mutanen gari sun shirya fitowarsu jiya amma shiru kake ji, wai ruwa ya ci makadi.

A karshe yaran da suka jefar da baburansu da jikkunan makarantarsu suka gudu da suka ga yansanda sun je wajen yansanda jiya rokon kayansu. Yansanda sun tsare su inda muka ce su sau su a karshe…bayan abinda ba a rasa.

Jimami

Abin ya zo wa y’an mazan da jimami mai yawa. Akwai yara maza da yawa da suka ce ba za su rika kwalliya da goge unifom ba saboda wadanda suke yi dominsu watau y’anmatansu ba su nan. Wasu ma sun yi barazanar barin makarantar.

A wata makaranta kam, bayan y’anmazan sun zo ranar Litinin suka ji abin banbarakwai don ba y’anmata, sai suka hada kai suka ki zuwa ran Talata. Na ce a tausaya musu, a ba su sati guda na jimantawa. Idan suka hakura, sati mai zuwa ko nan gaba sai a bude makarantar su ci gaba da karatu. Allah sarki! Yanmata kam sun koma Sa’adu Zungur GDSS. Sai dai a hakura. It’s really touching.

Muna ganin abun kamar wasa amma a gaskiya ko ni ne a wadannan shekarun aka raba ni da wacce muka shaku da ita ba zan ji dadi ba. Ko a kauye a da, a shekarun 1960s da early 1970s, Idan ka dawo daga makarantar boarding ka ji wata da kuke zumunci da ita an mata aure sai jimami ya kama ka. Balle wadannan yan birni. Mu sa kanmu a matsayinsu, mu taya su jimami. Ko soyayya ce ta kama ka a shekarun kuruciya, za ka yi ta ne bilhakki.

Tabbas, akwai wadanda suke daukan zumuncin har ya wuce intaha, ya kai ga abunda ba za a iya kyalewa ba kamar yanda muka fada kwanaki. Wadannan su kam, ba tausayawa. Ta faru, ta kare… Su hakura su je makaranta. In ba haka ba za ta b’are musu. In ba haka ba, abin zai yi yawa. Ga rashin yarinya, ga rashin ilimi? Da wanne za su ji nan gaba.

Godiya

Muna godiya ga kafatan din iyaye a jahar Bauchi da suka ba mu gagarumin goyon baya a kan wannan shirin. An yi ta yi wa Gwomnati fatar alheri da addu’o’i, har Gomna da muma an rab’a mu. Haka a wasu garuruwan da suka ji labari. Dubban masu karanta ni suma sun yi san barka. Madalla.

Allah ya datar da mu ga alherinsa, ya kara wa y’ayanmu fahimtar makaranta, ya shirye su da mu duka har zuwa ranar saduwarmu da shi.

Dr. Aliyu U. Tilde
Kwamishinan Ilimi
Bauchi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button