Binciken da aka gabatar an gano Kasashe 3 da su ka fi kowane mugun talauci a Duniya inda mutanen kasar suke shan wahala matuka.
A jerin dai ba a kawo irin su Kasar Sudan ta kudu da Yemen ba saboda halin tashin hankalin da Kasashen ke ciki.
1. Kasar Central Africa
Jamhuriyyar Kasar Central Africa ce kan gaba wajen fama da tsananin talauci inda sama da kashi 90% na kasar ke fama da yunwa da rashin muhalli. Kasar na fama da tsananin kazanta da matsalar rashin aikin yi.
2. Kasar Burundi
Kasar Burundi tana cikin wani mawuyacin hali inda sama da kashi 90% na kasar ba su da abinci kuma ba su iya mallakar $2 a duk rana ta Allah. Yanzu haka dai mutane da dama sun bar Burundi sun koma wasu Kasashen.
3. Kasar Congo
Kasar Congo tana gaba a wannan jeri duk da irin albarkatun da Allah yayi mata. Mutanen da ke more rayuwa a Kasar Congo ba su wuce kashi 1% cikin 100 ba. Bayan nan kuma kasar na cikin inda su ka fi hadari a Duniya.
An Sa Mata Zaga Gari Da Mijinta A Kafada Bayan Kama Ta Da Kwarto
Jama’ar gari sun tilasta wata matar aure daukar majinta a kafada ta zaga da shi a unguwa bayan an kama ta da laifin cin amanar aure.
Wannan abin ya faru ne a kauyen Borpadaw da ke kasar Indiya a farkon wannan wata da ake ciki.
Bayanai daga yankin sun nuna matar da lamarin ya shafa ta yi batar dabo na tsawon mako guda, lamarin da ya sa mijinta da surukanta bazama neman ta amma suka rasa.
Daga nan ne mijin ya kai rahoton bacewar matar tasa ga hukuma inda daga bisani wani ya kwarmata wa hukumar cewa matar na nan a gidan saurayinta.
Bayan an gano ta a gidan kwarton ne mijin ya fusata ainun wanda hakan ya sa ya lakada mata duka da kuma jan ta a kasa.
Bayan haka ne sai mutanen gari suka tilasta matar ta dauki maigidanta a kafada ta yawata da shi a cikin unguwa a matsayin horo kan abin da ta aikata.
An ga hoton yadda mutanen suka ciccibi magidancin suka dora shi ya zauna a kafadar matar.
Haka dai ta saba mijin nata a kafada ta yi yawo da shi yayin da jama’ar gari ke biye da ita.
Da alama dai wannan mataki bai yi wa hukumar yankin dadi ba, domin tuni aka damke wasu mutum tara da ake zargi suna da hannu cikin hukuncin, yayin da ita matar kuma an tura ta gidan iyayenta.