• Fri. Jun 21st, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Daga Karshe An Shiga Kotu Kan Shari’ar Fatima Wacce Aka Yankewa Kafa

ByLucky Murakami

Aug 29, 2022

An shiga kotu a yau Litinin domin sauraren shari’ar fatima wacce aka yankewa kafa sakamakon buge ta da mota.

Saidai kamar yadda amihad.com ta samu labari ‘yan uwan Fatima sun soma zargin ba za a yi musu adalci ba saboda yaron dan masu hali ne.

Hakan yasa suka fara tura kokensu zuwaga inda zasu samu taimako na bi musu hakkinsu.

A yau ne aka shiga kotu wajen zaman yanke hukunci ga wanda ya yi sanadiyar buge Fatima da mota, amma Alkalin kotun bai samu zuwa zaman na yau ba, saidai kuma an samu hargitsi wanda ya yi sanadiyar jami’an tsaro suka hana ‘yan jarida da sauran al’umma daukar hoto ko bidiyo a wurin.

A dalilin hakan ne wasu a bangaren Fatima suna zargin kotun da ba za ta iya musu adalci akan wanda ya yi sanadiyar buge `yar su ba saboda bangaren iyayen yaron masu kuɗi ne sannan kamar dai ana so a canza labarin.

Ya kamata jama’a ku fito domin mu nemi ‘yanci ga Fatima.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *