• Wed. Feb 12th, 2025

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Daga Karshe Bincike Ya Tabbatar Da Yan Matan Jihohi Biyu Da Sukafi Kwadayi A Nigeria

ByLucky Murakami

Aug 2, 2022

Barka da dawowa wannan shafi na amihad.com, a wani rahoto da wani mai yin bincike da sharhi kan sha’ani na zamantakewa da soyayya, ya nuna cewa ƴan matan da matan aure ƴan jihar Kaduna sun fi sauran matan yankin Arewacin ƙasar nan ƙwaɗayi da sin abin hannun mutane.

Bisa ga wannan rahoto, matan da ke jihar Kaduna sun fi son saurayi ya basu ƙudi da abin hannun sa idan har yana so ya samu damar su su rika sauraran sa.

” Idan a Kaduna kake neman mace ko da aire ne, babban burin ta shine ka zamanto mutum mai kuɗi sannan kuma mai kashe su yadda ya kamata. Cikin Ɗan kankanin lokaci za ka ga suna bin ka kamar ƙudan zuma.

Da yawa daga cikin matan Kaduna sukan fi zaman aure ne idan mazajen su masu hali ne, idan kuwa ba haka ba, kun dinga samun matsala da iyalin ka kenan.

Jiha ta biyu dake bi mata, ita ce jihar Katsina.

Suma ƴan matan jihar Katsina irin wannan tafiya suke yi. Dama kuma ƴan biyu ne masu kama ɗaya.

” A jihar Katsina, sai kana da abin hannu fa. Idan ba haka ba gaskiya rike mace zai yi maka wahala a wannan zamani. Domin muna da ‘taste’” in ji Hindatu Sani.

Jihar Jigawa, Bauchi da Gombe, sune ke can kasa a teburin wanda matan su ba su damu da aljihun ka ba, soyayyace suka fi damuwa da ita.

” Mu a yankin mu idan na miji ya nuna maka tsantsagwaran soyayya, ya ishe mu ba sai ka tara maƙudan ƙudi ba.

Su ko Kanawa kuɗin ka bai dame su ba, idan suna sonka shike nan.

” Ƴan matan Kano sai su yi maka hanyar arziki ma idan har suna ƙaunarka ba sai ka zo musu da buhunan kudi ba.

” Babban abinda suka fi shine mace kyakkyawa fara, burin bakane kenan. Shi dai ace matar sa fara ce tas-tas, son kowa kin wanda ya rasa. ”

Wannan Rahoto na bincike da aka yi a kan wasu bangare na mata dake wasu daga ciki jihohin Arewacin Najeriya.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *