• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Daga Karshe Sheikh Bello Yabo Yayi Zazzafan Martani Zuga Yan Kannywood Akan Wannan Sabon Abu Da Suka Fito Dashi

ByLucky Murakami

Aug 31, 2022

Kamar yadda mukaci karo da bidiyon shahararren malamin addinin muslunci nan na arewacin Nigeria mai suna Bello Yabo Sokoto yayi wani zazzafan martani akan wasu jaruman kannywood wanda suke hawa wakokin mawaki ado gwanja da chass da kuma warr saboda yadda ake fitsara akan wa’yannan wakokin.

Kamar yadda kuka sani dai malamai sun saba maida martani akan abubuwanda suka ga anyi wanda basu dace ba, musamma masu bata tarbiya.

Sannan suna tabbatar da inda addini yayi hani akan irin wadannan abubuwa da kuma yiwa mutane nasiha da su dai na abubuwan da basu dace ba.

Malamin yace duk wacce akaga tana hawa wannan wakar kuma tana rawa ta rashin mutunci to hakika wannan mutuniyar banza ce bata da tarbiyya kuma yakamata asa jami’an tsoro su kamata.

Sannan malamin ya kara kira ga hukuma cewa indai har tana kishin tarbiyar yaya Musulmi mata to ya kamata a dauki mataki akan wannan abubuwan da jatumai mata na kannywood suke yi.

Sannan ya kara da bayyana sunayen manyan jarumai masu bata tarbiyar na cikin masana’antar kannywood.

Gadai bidiyon nan zamu gabatar muku a kasa sai kulla kuji daga bakin mallam.

https://www.youtube.com/watch?v=PXrAq2_EFdQ

Sai ance daman wannan malamin baya rabo da zagi da kuma suka akan yan kannywood kai harda ma sauran malamai yan uwansa bai barsuba dan babu wani malami daya bari balle yan film.

Sai dai kuma na ganin kokarin malamin ganin yadda ya fadi gaskiya akan wannan abu domin duk wani me kishin yayansa to zaiyi fada da wannan abun daya fito na wakar chass.

Ya kamata a dinga sanin irin abubuwan da za’a nayi wanda basu saba shari’a ba musamman shari’ar addini.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *